Tuesday 11 September 2018




Shugaba Buhari :- Za mu ci gaba da tatse dukiyar al'umma a hannun barayin gwamnati

Home Shugaba Buhari :- Za mu ci gaba da tatse dukiyar al'umma a hannun barayin gwamnati

Anonymous

Ku Tura A Social Media

 A ranar Talatar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, gwamnatin sa ta dukufa gami da tashi tsayi irin na tsayuwar daka wajen tatse dukkanin wata dukiyar al'ummar kasar nan daga hannun barayin gwamnati.


A yayin bayyana wannan lamari na tatso dukiyar al'umma a matsayin wani tafarki na yakar cin hanci da rashawa, shugaba Buhari ya kuma yi kira ga majalisar dokoki ta tarayya akan daukar matakan shigar da sabuwar dokar hukuncin miyagun laifuka a kasar nan. Yake cewa, muddin wannan sabuwar doka ta samu shiga a kasar nan za ta kawo wani yanayi na juyin juya hali da zai saukaka tatso dukiyar al'umma daga hannun barayin gwamnati. Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a fadar gwamnatinsa ta Villa yayin karbar rahoton binciken kwamitin mutum uku da ya kafa masu kididdiga kan tatso dukiyar gwamnati da al'ummar kasar nan.

Shugaban kasar a ranar 22 ga Nuwamban 2017, ya assasasa wannan kwamitin na mutum uku da ya hadar da; Mist Olufemi Lijadu, Mrs. Gloria Chinyere Bibigha da kuma Mista Muhammad Nami.

NAIJ.com ta fahimci cewa, shugaba Buhari ya sahalewa wannan kwamiti kan gudanar da duk wata kididdiga da binciken dukiya a cibiyoyi da ma'aikatun gwamnatin tarayya tun daga ranar 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 22 ga watan Nuwamba na shekarar da ta gabata.


A ranar Talatar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, gwamnatin sa ta dukufa gami da tashi tsayi irin na tsayuwar daka wajen tatse dukkanin wata dukiyar al'ummar kasar nan daga hannun barayin gwamnati. A yayin bayyana wannan lamari na tatso dukiyar al'umma a matsayin wani tafarki na yakar cin hanci da rashawa, shugaba Buhari ya kuma yi kira ga majalisar dokoki ta tarayya akan daukar matakan shigar da sabuwar dokar hukuncin miyagun laifuka a kasar nan. Yake cewa, muddin wannan sabuwar doka ta samu shiga a kasar nan za ta kawo wani yanayi na juyin juya hali da zai saukaka tatso dukiyar al'umma daga hannun barayin gwamnati. Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a fadar gwamnatinsa ta Villa yayin karbar rahoton binciken kwamitin mutum uku da ya kafa masu kididdiga kan tatso dukiyar gwamnati da al'ummar kasar nan. Za mu ci gaba da tatse dukiyar al'umma a hannun barayin gwamnati - Buhari Source: Twitter Shugaban kasar a ranar 22 ga Nuwamban 2017, ya assasasa wannan kwamitin na mutum uku da ya hadar da; Mist Olufemi Lijadu, Mrs. Gloria Chinyere Bibigha da kuma Mista Muhammad Nami. NAIJ.com ta fahimci cewa, shugaba Buhari ya sahalewa wannan kwamiti kan gudanar da duk wata kididdiga da binciken dukiya a cibiyoyi da ma'aikatun gwamnatin tarayya tun daga ranar 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 22 ga watan Nuwamba na shekarar da ta gabata. KARANTA KUMA: Atiku ya yi kaca-kaca da Shugaba Buhari kan watsi da sauya fasalin kasa a jihar Kano Kawowa yanzu shugaba Buhari bai bayyana sakamakon binciken da wannan kwamitin ya gudanar, sai dai ya sha alwashi na dabbaka duk wani mataki da hukunce-hukuncen da suka dace a kai. Kazalika shugaban kasar ya bayyana rashawa a matsayin wata mummunar barazana ga tsaro gami da tattalin arzikin kasar nan tare da shan alwashi kan cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da jajircewa wajen kawo karshen wannan barazana a kasar nan. 

Share this


Author: verified_user

0 Comments: