Wednesday, 5 September 2018




APC Sokoto sun tsayar da Shugaba Buhari 2019

Home APC Sokoto sun tsayar da Shugaba Buhari 2019

Anonymous

Ku Tura A Social Media

Kasa da makonni uku kafin zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress ( APC ), mambobin jam’iyyar babin jihar Sokoto sun tsayar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takaran da suke so ya samu tikitin jam’iyyar.
Haka zalika, jam’iyyar ta nuna amincewarta ga shugaban kungiyar sanatocin arewa, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko sannan sun bayyana shi a matsayin shugaba guda a jihar.
Wannan hukunci na daga cikin matsayar da suka tsaya kai a karshen taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a Sokoto a ranar Talata, 5 ga watan Satumba wadda ya samu halartan shugabannin jam’iyyar a jihar, da masu ruwa da tsaki jam’iyyar.


Mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Ahmed Aliyu Sokoto ne ya jagoranci ganawar wadda aka gudanar cikin sirri, inda ya bayyana Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a matsayin uban jam’iyya nagari aa jihar.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanya ranar zaben fidda gwani na shugaban kasa domin zabar dan takaranta a zaben shugaban kasa na 2019.
Kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sunce zaben fidda gwani na jam’iyyar mai mulki zai gudana a ranar Alhamis, 20 ga watan Satumba.
Jam’iyyar a tsarin gudanarwan ta tace za’a samar da dan takarar shugaban kasa ta hanyar zaben fidda gwani wato “direct” kenan a turance.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: