Thursday, 28 December 2017




Al’amura 3 da suka jawo cecekuce a farfajiyar Kannywood a 2017

Home Al’amura 3 da suka jawo cecekuce a farfajiyar Kannywood a 2017

Anonymous

Ku Tura A Social Media

A daidai lokacin da muke shirin shiga sabuwar shekara, NAIJ.co tayi amfani da wannan dama domin kawo masu wasu daga cikin abubuwan da suka faru a farfashiyar shirya fina-finan Hausa na Kannywood.

Daga cikin takaddamomi uku da aka fuskanta da dandalin akwai:

1. Adam Zango

Adam Zango na daya daga cikin fitattun jaruman Kannywood da suka yi fuskanci yan matsaloli a farfajiyar.

Idan bazaku manta ba a watan Nuwamban wannan shekarar, Adam Zango ya fito a fusace inda ya kalubalanci dukkanin masu cewa wai yana yin tsafi da kuma harkar bin maza.

Adam ya nuna fushin sa a shafinsa na ‘Instagram’ akan al'amarin sannan kuma ya gargadi jama’a da su daina haka ko kuma su sa kafar wando daya da shi.

2. Ummah Shehu

Ita kuma Umma Shehu an zarge ta ne da rashin samun ta ingantaciyyar ilimin adinin musulunci.

Anyi ta kumfar bakin tun bayan tabargazar da ta yi a wata hiran da Momoh na gidan Talabijin din Arewa 24.

Momoh ya yi mata wasu ‘yan tambayoyi ne game da adinin musulunci wanda mutane basu gamsu da shi ba.

3. Rahama Sadau


Rahama Sadau ma ta fuskanci gagarumin matsala da kushe bayan bayyanarta a wani bidiyon waka tare da wani mawaki mai suna ‘Classiq’ a 2016 ne farkon sanadiyyar matsalolin da Rahama Sadau ta yi fama da su a farfajiyyar fina-finan Hausa har a 2017.

Sakamakon haka ya sa Rahama ta rubuta wa kungiyar MOPPAN wasikar neman afuwa game da dakatar da ita da akayi.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: