Thursday, 1 March 2018




Dan Adam

Home › › Dan Adam

Anonymous

Ku Tura A Social Media
Dan Adam

Jiki na rawa take kwankwasa k'ofar d'akin da k'arfi tana fad'in.
"Habiba! Ke Habiba!"
"Na'am." Ta furta cikin magagin bacci kafin ta mik'e ta bud'e d'akin. Ganin aminiyarta Saude ne ya sanyata wartsakewa babu shiri. Ta waro ido. "Lafiya dai Saude?"
Saude ta rage murya.
"Ina fa lafiya? Ga waccan shegiyar tana nak'uda. Ai idan ta haihu na kad'e."
Habiba ta dafa kafadarta.
"Karki damu, ai idan har ni ce unguwar zoma ba zata haife d'anta da rai ba. Itama muje sai ta bar duniya."
Wani sanyi ya mamaye zuciyarta. Habiba ta dauko kayan amfani ta yi gaba Saude na biye da ita. Lokacin karfe shida na safe.
Acan suka iske Malam Balarabe yanata faman zirga-zirga a tsakar gidan. Shigowarsu ne ya sanyashi nufarsu da saurinsa.
"Yauwa, Habiba don Allah taimaka mata."
"Ka kwantar da hankalinka Malam Balarabe, in sha Allahu lafiya kalau zata sauka. Ka sama mana itatuwa dai na dora ruwan zafi.
Daga haka ta shiga ciki, Saude na gefe tana matsar kwallar munafunci ita a lallai tausayin abokiyar zamanta takeyi. Da ire-iren kissar da take cin galabar Malam Balarabe kenan. Da sauri shi kuma Malam ya fice.
Saude dake tsaye sai jin kukan jariri tayi. Gabanta ya bada ras ras! A gigice ta fad'a d'akin. Bakinta na rawa ta tambaya. "Ta..ta.." Ina maganar gaba daya ta mak'ale a saman le66anta.
Habiba ta dubeta tayi mata alama da tayi shiru. Dole ta rufe bakinta ba don ta so ba.
Habiba ta kammala yanke cibi ta mik'awa Saude d'iyar. Saude cikin kukan bakin ciki marar sauti ta kar6eta tana ji kamar ta shak'eta ta mutu.
Ga mamakin Saude, Habiba filo ta dauko ta danne fuskarta da shi, tun Hasiya na shure-shure har tayi lakwas. Saida ta tabbatar da cewar ta cika sannan ta yi jifa da filon ta mik'e tana sharce gumi.
Saude jikinta babu inda baya rawa.
"Ta mutu." Ta fad'a a gigice.
Habiba ta gyada mata kai sannan ta dubeta.
"Eh na cika burinki. Yanzu Malam na dawowa mu nuna mutuwa tayi bayan ta haife d'iyarta. Ko kusa kada ki nuna wata alama ta rashin gaskiya Habiba. Ita kuma wannan k'aramar alhaki ce, ni nasan yanda zamuyi da ita nan gaba kadan."
Saude ta amince da batun aminiyarta.
"Shikenan."
Ai kuwa sunajin sallamar Malam suka hau salati da koke-koke.
Malam baisan sadda ya yarr da itatuwan da ya riko ba. Jiki na rawa a gigice ya fada dakin yana tambayar ko lafiya.
Ya dubi Saude hannunta rike da jaririya tana ta canyara ihun kuka kafin ya kai dubansa ga Habiba. Bai yi wata-wata ba ya yi kan Hasiya yana kiranta a rud'e.
"Hasiya! Hasiya!!"
Ina! Ya fahimci abinda ake nufi, Hasiya ta rasu. Ya hau salati yana zubda ruwan hawaye. Baice uffan garesu ba ya fita zuwa tsakar gida ya zauna.
* * *
Haka yana ji yana gani aka wanke Hasiya aka kaita gidanta na gaskiya batare da 'yan uwanta sun sani ba saboda nisan dake tsakanin garuruwansu.
Malam Balarabe ya shiga tashin hankali matsananci, ya rame yayi bak'i kamar ba farin mutum ba. Ga duk wanda ya ganshi dole ya tausaya mishi musamman abokansa wadanda suka riga sukasan irin kaunar da yake yiwa matarsa Hasiya don kuwa baya 6oyemusu irin yanda take kyautata mishi a rayuwa ta hanyar yin biyayya ga dukkanin umarninsa.
Sai ranar bakwai sannan babban yayan Hasiya da kuma mahaifiyarta da sauran yayyunta uku mata suka iso. Sun koka kwarai da rashin yar uwarsu. Saidai babu yanda suka iya, su mutane ne wadanda sukasan ya kamata, sam basu zargi komai ba. Toh me zasu zarga? Bayan sun san irin kaunar da Saude ke nunawa Hasiya a gabansu tamkar ba kishiyarta ba. Wannan ne yasa koda Saude tace zata rik'e yarinya, babu wanda baiyi na'am ba. Haka suka tattara suka koma garinsu batare da shakkar komai ba.
* * *
Wahala, tsangwama da kyara, babu irin wacce d'iyar Hasiya, wacce ta ci sunan mahaifiyarta Hasiya suke kiranta da Ummi, bata gani ba wajen Saude. Saidai a gaban idon Malam Balarabe, babu abinda Saude bata yiwa Ummi na nuna kulawa da kauna. Yarinya ce mai hakuri, haka take hakura da komai ta shanyeshi, anan ma Mahaifiyarta ta dauko.
Saida ta kai shekaru goma sha uku a duniya sannan Saude ta samu ciki. Zo kaga murna wajen Saude da mijinta. Sai ya zamana bayan Saude ta haifi diyarta Mariya. Ta chanja kwarai a gidan. Ta hanyar asiri da tsafi, ta siye zuciyar Malam Balarabe ya zamana ko kallon Ummi baya kaunar yi. Komai ya samo, daga Saude sai Mariya. A wannan lokacin ne, Habiba ta zo da shawarar tura Ummi aikatau. Ba musu ba jayayya, Malam Balarabe ya amince da a turata ko bangon duniya ne. Duk acewarsa, bashi da matsala ko wata damuwa...!

Dan Adam

Share this


Author: verified_user

0 Comments: