Gwamna Masari Ya Yi Ganawar Sirri Da Fati Muhammad (karanta kuji)
Rahoton Katsina Post Hausa
Shararriyar Yar fim din nan Mai suna Fati Muhammad ta je Katsina inda tayi wata ganawar sirri da gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari. 'Yar wasan wadda yanzu ita ce babbar jakadiyar tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar wanda yake neman tsayawa takarar shugaban kasa karkashin jam iyyar Adawa ta PDP.
Bincike ya tabbatar da cewa yar fim din ta kwashe kwanaki a wani otal din Katsina inda kuma wani daga cikin ma su taimakawa Gwamnan ya rika dawainiya da ita. Haka ma dai mun samu cewa daga karshe ta samu ganin Gwamnan amma babu wanda ya san me suka tattauna a tsakanin su.
Majiyar ta mu har ila yau ta bincika ta kuma tabbatar cewa ganawa bata ofis bace, shi yasa ma ba a ga Fati Muhammad din a ofis ba, amma ganawa ce ta kashin kai.
“Zuwan na Fati Muhammad Katsina yafi alaka da siyasa bana wasan fim bane.” Kamar yadda muka samu.
Domin duk ‘yan fim din Katsina babu wanda ya san ta shigo, kamar yadda bincike Taskar labarai ya tabbatar. Wani Dan fim yace zirga zirgar Fati Muhammad yanzu tafi dangantaka da siyasa fiye da harkar fim Kuma kwananan shafin ta na Facebook ya yi kaurin suna wajen sukar salon mulkin shugaba Buhari, wannan yasa ganinta a Katsina don ganin Gwamnan zai ba kowa mamaki.
Jaridar Katsina Post Hausa sun Aikawa Fati sakon wayar Hannu har zuwa rubuta rahoton nan bata bada amsa ba wani jami’in gwamnatin Katsina yace shi bai san zancen ba.
0 Comments:
Post a Comment