Friday, 4 May 2018




Fitaccen Mawakin Kannywood Nazir Ahmad Sarkin Waka Ya Tabbatar Da Cewa Yana Soyayya Da Jaruma Hadiza Gabon

Home Fitaccen Mawakin Kannywood Nazir Ahmad Sarkin Waka Ya Tabbatar Da Cewa Yana Soyayya Da Jaruma Hadiza Gabon

Anonymous

Ku Tura A Social Media


Fitaccen mawakin hausa na kannywood Naziru Ahmad, ya bayyana ainihin alakar da ke tsakaninsa da shahararriyar jarumar Kannywood, Hadiza Gabon a cikin wata hira ta musamman da jaridar Aminiya ta yi da shi.


Mawakin ya bayyana cewa suna soyayya da juna kuma suna matukar son juna a lokacin da Jaridar ta tambaye shi menene ainihin alakarsa da jaruma Hadiza Gabon.

Naziru ya cigaba da cewa: “Mutum ba zai ce ya yi asara idan yana soyayya da ita ba. Amma a zahirin gaskiya ba a sa ranar aurenmu ba, komai na Allah ne”- Inji shi.

A yayin tattaunawar mawakin ya musanta batun da ke yaduwa na cewa wai gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bashi kyautar kudi naira miliyan 50 biyo bayan wata waka da yayi masa, inda yace ba gaskiya bane, “Amma ba zan bayyana abinda ya bani ba.” Inji shi.

Da mawakin ke karin haske game yadda ya tsunduma waka, ya bayyana cewa ya fara waka ne a shekarar 2002, inda yace zuwa yanzu yana hasashen adadin wakokin da ya rera a tun bayan fara waka gadan gadan sun kai 300.

Daga karshe ya bayyana cewar duk a cikin wakokinsa ya fi kaunar wakar ‘Dan Adaln Mubi’ da kuma ‘Sardaunan Dutse’, musamman saboda a cewarsa duk abinda ya fada a cikin wakar ya gansu a zahiri, wasu kuma ya ji su.

Daga shafin al'ummata.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: