Wednesday, 4 July 2018




SO NE.. PART 4

Home SO NE.. PART 4

Anonymous

Ku Tura A Social Media


Na tashi da sauri naje na dauki wayata na duba domin naga waye ke kirana, sunan Fatima na gani alamar cewa itace ke kirana, na daga kiran tare da kara wayar a kunnena nayi sallama, cikin tattausar murya Fatima ta amsamin tare da cewa 'Abba kawuni lafiya' na amsa mata da 'lafiya' kafin na kara cewa wani abu sai tacemin 'Abba narokeka da ka amsamin da kanasona idan ba haka ba zan fada mawuyacin hali, tabbas son ka ya kai girman da bazai iya fita daga zuciyata ba, domin bazan iya bacci ba sai naji muryarka, a duk lokacin da nake jin lafazinka yakan karamin karfin gwiwa, duk wata damuwa da nake ciki nakan manta da ita a duk lokacin da nake magana dakai, yaya na na durkusa bisa gwiwoyina ina rokonka da ka karbi soyayyata kada na fada wani hali'.
A lokacin ne naji wani abu ya soki zuciyata wanda na kasa ganewa menene, na danyi shiru sannan nace da Fatima 'kanwa ta kada ki jefa kanki cikin wani hali akan soyayya, kuma inaso ki sani cewa komai nufine na allah, idan ya nufa zaki zama matata to ba abinda zai hana, idan kuwa yayi nufin bazaki zama matataba to ba yadda za'ai na aureki, kuma furta soyayyata a gareki ba zai tasirin komai ba'.
Cikin wata murya mai sanya tausayi Fatima tace dani 'yaya Abba idan har ban aureka ba mutuwa zanyi, nidai burina ka amince da soyayya ta kuma ka kaddara a ranka zan zama matarka da yardar allah' na amsa mata da cewar 'idan allah ya nufa kece mata ta sai ince allah yasa hakan shine mafi alkhairi, idan kuma...'
Fatima ce ta dakatar dani kafin na karasa fadin magana ta da cewar 'yaya Abba banaso naji kana fadamin wani abu da ya danganci rabuwarmu da kai saboda idan har hakan ta faru to zan rasa rayuwata'
Haka muka shafe a kalla awa guda muna magana da Fatima amma bata nunamin alamar zata hakura da kiran ba, sai nine na cemata 'Fatima ya kamata ki kwanta saboda dare yayi' haka mukai sallama da ita amma sai taki katsewa kiran sai nine na katse kiran sannan na ajiye wayata na kwanta da tunanin Fatima a zuciyata, aikuwa kwanciyata ke da wuya sai bacci ya daukeni..

Share this


Author: verified_user

0 Comments: