Tuesday, 3 July 2018




Tun awanni hudu kamin mu buga wasa da Argentina na samu labarin sace mahaifina amma dan kada in ba 'yan Najeriya kunya hakanan naki gayawa kowa labarin naje na buga wasan>>Inji Mikel Obi

Home Tun awanni hudu kamin mu buga wasa da Argentina na samu labarin sace mahaifina amma dan kada in ba 'yan Najeriya kunya hakanan naki gayawa kowa labarin naje na buga wasan>>Inji Mikel Obi

Anonymous

Ku Tura A Social Media


Labarin sace mahaifin tauraron dan kwallon Najeriya, Mikel Obi ya karade kusan ko'ina a kasarnan, inda aka samu cewa wasu masu garkuwa da mutane sun sace mahaifin nashi a lokacin da yake kan hanyar zuwa Enugu daga Jos.

Mikel Obi ya bayyana cewa, labarin satar mahaifin nashi ya zo mishine awanni hudu kamin fara wasan Najeriya da kasar Argentina, sun bukaci a basu miliyan goma kuma sunce kada a gayawa 'yan sanda idan ba haka ba zasu kashe mahaifin nashi, kamar yanda ya gayawa, KweseESPN.

Obi ya kara da cewa, ya shiga tashin hankali amma sai bai gayawa kowa ba, abokan wasanshi, shuwagabannin hukumar kwallo ta Najeriya da ma me horas dasu, Gernot Rhor duk babu wanda ya gayawa.
Yace yayi hakane dan kada ya dauke hankulan 'yan wasan bisa muhimmin wasan da zasu buga da kasar Argentinar, haka ya daure yaje ya buga wasan dan kada ya baiwa mutanen Najeriya miliyan 180 kunya, kamar yanda ya bayyana.

Rahotanni sun bayyana cewa Mikel na shirin fitar da mahaifinshi kasar waje dan a kara kula da lafiyarshi.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: