: KYAUTAR BUDURCI
KYAUTAR BUDURCI PART 1 Ra'uf,Rabi'u, da Ridwan Yan uwan juna ne,uwar su daya ubansu ,ra'uf ne babba ,sai rabi'u sai ridwan ,yan asalin jihar misau ne ,sunyi karatun boko da arabi,amma ra'uf da rabi'u sun fi yin xurfi a boko,yayin da ridwan ya maida hankali a gonarsu ta gado ,domin yana gama secondary yayi aure ,ya shachi bangare a gdansu ya xaune da matarsa hauwa ,bayan shekara uku da aurensu su ka haifi 'ANWAR' , a lokacin rabi'u yayi aure da matars ramla ,bayan ya samu aiki a NNPC ,shima ya tare birnin abuja ,shekara biyu da auransu suka haifi 'ANAS', Rau'f baban boko shi medicine ya karanta ,shine dai auren nasa daga baya baya , bayan kuma shine babba,ya kamalla karatunsa ya samu zama consultant a asibitin AKTH ,ya tamfatsa gdansa a darmanawa ya tare da matarsa yar asalin kuwait' girman kano amma mai suna 'lubna'........zuwa yanxu anwar na da kanne uku adam,basma da bahijja ,yayin da anas yake da kanwa guda daya aisha .......ra'uf,rabi'u ,ridwan dukkansu suna yin zumunchi mai tsafta ......... Duk da kowa garin da yake daman , ra'uf da lubna sai da suka shekara biyar da aure ALLAH ya azurta su ya mace ,ranar suna aka sa mata suna 'zARINA' ........daga kanta lubna bata qara haihuwa ba,duk wani so da gata sai suka dorawa tilon yar su zarina............BAYAN SHEKARA 16... PART 2 'ANWAR RIDWAN' ,saurayi kyakkyawa na ajin farko,miskili,nagartacce,dan gaye ,mai tsafta ,dan kimanin 23 ,ya gama poly dinsa .....yanxu haka ya samu admission BUK sun bashi lvl 2 ,course din business admin .....yau yake shirin barin misau izuwa kano ,xai xauna a gdan yayan mahaifinsa Alh.Ra'uf,domin shine ya sama mai admission ......... 'ANAS RABIU' .....dan hutu ,dan gata ,mutanen abuja .....saurayi mai ji da class da charisma ,dan kimanin 20......ana kasar 'holland' ana hada deegree......... 'ZARINA RA'UF' shalelen iyayenta,kyakkyawar gaske ,wanda kyanta ya samo asali gun mahaifiyarta domin tama dara haj.lubna a kyau ,ga gashi ,ga iya kwalliya ,duk gatan ta hakan bai sa ta sangarche ba ,tana tarbiya dai dai gwargwado,yanxu haka tana kan kuriciyarta wato 'sweet 16' ,amma in ka ganta sai ka rantse she's 18 saboda garin jiki,tana ss3 yanxu haka........ Anwar ya iso kano lfy ,ya doshi gdan 'aljannar duniyar ' uncle dinsa Alh.ra'uf ,tarba iya tarba ya samu ,domin hajiya lubna ,macece mai son jama'a ,bayan an kaishi dakinsa ya natsa ,domin lokacin da yazo zarina na skool , yana kwance kan gado yana hutawa ........a wannan lokacin zarina ta dawo tana part dinta abunta ,.domin yanayin garin akwai hadari,ruwan sama at any time,....ruwan sama akayi sosai ,zarina mayyar ruwa ,ta faki idon mahaifanta ta nufi garaji ta fara wanka da ga shimi sai 3qtr a jikinta ,tana wanka tana tsalle, hakan yayi dai dai da anwar ya zo yarufe windon dakinsa domin ruwan dake shigowa ,tsayawa chak yayi tare da rintse idanunsa yayi ,domin wani kibiya da ya soki xuciyarsa ,hakan ya haifar mai da wani shock . Dalilin hango beautiful Zarina dancing in the rain ...........a takaice dai Anwar an kamu .. : KYAUTAR BUDURCI : KYAUTAR BUDURCI PART 3 Anwar cikin ikon Allah ya fara zuwa makaranta,bayan an mallaka masa mota (driver ya koya masa)tsakaninsa da zarina gaisuwa ......suna jin dadin zama dashi,ba ruwan shi da tsabgar kowa ,wato baida zaqewa ,yana kama kansa sosai.........a yau alh.ra'uf ya damqawa anwar amanar sauke zarina a skul kafin ya wuche tasa makarantar ,hakan ya janyo shakuwa mai tsanani a tsakaninsu ,amma miskilanchin anwar bai sa zarina ta harbo jirgin son da yake mata ba,ya bar wa xuciyarsa ,ita kanta zarina ta yaba da anwar ,sai ta xauna tayi ta tunaninsa,in basu hadu ba ,tayi ta kewarsa ,hakan na nuni da ce wa ta kamu amma ita kanta ba ta sani ba .....ranaku ,satittika ,watanni sun shude .......shekara ta bada baya ....zarina an kamalla secondary ......anwar an lvl 3 ,zuwa yanxu duk su biyun sunyi tsamo tsamo cikin tafkin tekun soyayyar junansu ......amma sun boyewa junansu ........sun damu da junansu matuqa ,komai tare ,irinsu chin abinci ,fita shopping ,qarin karatun qur'ani da litattafan addinni......da sauransu ......ra'uf da lubna sun dau haka a matsayin haduwar jini ,zallar kauna da yan uwan taka ................ A yau Zarina ta cika shekara 18 , ta zama cikakkiyar BUDURWA ,komai ya ji........ Hijabs sune abund zarina take sakawa ,bisa umarnin yayanta kuma masoyinta anwar ...... Anwar yana lvl 4 ynxu wato final year ,zarina kuwa an fara zuwa CAS ....... Yau Anwar ya shirya leqawa misau kamar yadda ya saba duk karshen wata ....alh.ra'uf ya hada mai tsarabar da zai kai wa ridwan wato kanninsa....... ..zarina hankalinta a tashe duk tayi narai narai da idanu ....anwar ya dubeta ya ce sweetsis kwana 10 kawai xanyi in dawo ,ga waya ,ga whatsapp we will kip in touch, ta dubeshi da fuskar shagwaba, amma yaya kasan zanyi missing dinka sosai,gdan xai yi min fadi wit out u .....da kyar anwar ya lallasheta yayi tafiyarsa .....suna masu kewa da begen juna ............ ANAS ne tsaye a filin airport din nnamdi azikwe dake abuja ,an dawo daga holland tare da kwalin degree ..... [: KYAUTAR BUDURCI PART 4 Iyayensa da 'kanwarsa aisha,suka tarbeshi,suka wuce gida cike da murnar dawowarsa,bayan kwana uku,alh.rabiu ya cewa anas ya shirya zasu tafi kano gaba d'ayansu daga kano su wuce misau,domin sada zumunci.. Yau tunsafe ake shiryen shiryen isowar alh.rabiu da iyalansa,karfe 5pm suka iso ,sai murna ake,anas kuwa idanunsa na kan zarina ,domin ta mugun tafiya da imaninsa,karfe takwas bayan sun kimtsa,ana kan dinning ana cin dinner,zarina tana kitchen tana had'a citrus salad,anas ya dubi dad dinsa,yace ni fa naga mata a gidannan,alh.rabiu yace ga ka ga babanka ,saika gaya mashi,alh.ra'uf ya d'ago yace menene d'ana,anas yana sosa kai yace zarina nagani kuma nake so,alh.ra'uf ya murmusa yace da kai da ita duk daya a guna,anas na baka zarina,ko bayan raina ina mai bada wasiccin aurenku kai da zarina,hakan yayi dai da sulalewar glass bowl daga hannun zarina,mai dauke da citrus salad ....tirkashi PART 5 Tashin hankalin da zarina ta shiga bazai kwatantu ,a take ta tattaro nutsuwarta ta juya ta bar gun .......... Tun daga ranar ta kauracewa kowa a gidan ,ta kulle kanta a daki ,in banda kuka ,bbu abinda takeyi,sallah ma da kyar take rarrafawa tayi,ta rufe duka wayoyinta ,in kaga tafito abinda xa ta kai bakin salati taje nema a kitchen..... Anas kuwa murna yake abun sa ,ya samu abunda rai ke so,matsalarshi daya ,rashin ganin zarina ko da a dining ne ,ita kanta aishar ba haduwa suke da zarina ba balle yasa ran chusa kansa ko ta bangaren kanwarsa ne...a nashi ganin wai kunya ce ta hanata fitowa ,take gudunsa....... Alh.ra'uf da rabiu shagalin gabansu kawai suke ,domin Alh.ra'uf ya bugawa mal.ridwan waya cewan yana buqatar yazo kano tare da iyalensa .....ana san ran yau zasu ma zo...... Haj.lubna ta dubi zarina 'lafiarki kalau kuwa ,kin hana kanki walwala ,ba kya fitowa , ki kunshe kanki a daki,in ma lamarin auren nan ne yasa kika maida kanki haka,toh gwara ki cire damuwa a ranki ki rungumi aurennan ,domin ko datsewar numfashinki ba zai sa hana aurennan ba ,ko gawarki ne sai a wanke an kai ,ke in banda abinki banga kina kula wani ba,domin ko kare ban taba ganin yaxo gunki ba .....ko kina da wanda kikayi wa alkawarine ? ....shirun da zarina tayi ya bata daman cigaba da magana da sigar lallashi ta dubi zarina' kiyi hakuri ,ki zama mai juriya da rungumar kaddara,ki yi biyayya ,zarina kiyi biyayya ki rabu damu lafiya kinji........... Ta dubi kofar da umman ta fice ,sai kawai ta fashe da wani kuka mai ciwo, anwar kai nake so,kaine farin cikina .akan ka nafara sanin so ,akanka nasan dadin zama da masoyi ,akanka nasan menene unconditional love,anwar meyasa baka fadawa abbanka kana sona ba,meyasa baka furta min so ,meyasa baka nunawa duniya kana sona ........toh sakarya shi ce miki yayi ya na sonki,daga yace zai furtamiki muhimmiyar kalma ,sai ki dauka sonki yake ,haba zarina ki tsai da hankalinki ,ki nutsu ....zuciyarta ta nussasheta........shigowar su aisha,basma da bahijja ya dawo ita daga tunanin da ta fada ......ta dubesu ......hakan na nuni anwar da yan gidansu sun iso kenan ........nima na bisu da kallo domin b3 na yayi low... : KYAUTAR BUDURCI PART 6 Zarina ta kokarta ta saki jikinta ,ta fito ta gaisa dasu kawo ridwan,aka hallara a dining karan cokali kawai ake ji,anwar sai neman idon zarina yake ,amma ita tasha mur 'domin ita haushinsa takeji ,anas kuwa bakinsa uwa gonar auduga,sai fara'a yake ........... Bayan sallar isha kowa ya hallara falo (familyn so cute) .... Alh.ra'uf yayi gyaran murya ...yace abunda yasa muka taru anan gaba dayan mu shine,nariga na yanke hukuncin za'a daura auran ANAS da ZARINA ,ANWAR da AISHA ...ranar juma'ar nan domin abu ne tuwo na mai na ,aisha xata zauna anan ,zarina zata bi angonta Abuja, Anwar saboda miskilanci baza ka iya gane a wani hali yake ba , Anas kuwa sai hamdala yake a zuci , aisha kuwa ko a jikinta ,domin anwar ba mijin yadawa bane ,zarina kuwa sharce hawaye tayi wayance ta duban anwar (anata ganin kamar bai damu ba) ...... Alh.ra'uf ya ce akwai mai magana ? ,kowa yayi tsit....haj.lubna ta muskuta tace Alhaji anya ba'a yi gaggawa ba ,i da ka bari anyi shiri sosai ,ya dubeta yace 'ni fa na gama magana ,ina damar in aurar da yayan ,kuma bahijja da basma na baku wata daya ku fito naku mazajen , kowa na iya tafiya ,...... Iyaye mata suka nufi dakin haj.lubna domin fara tattaunawa akan shirye shiryen biki ...... Iyaye maza kuwa restroom din Alh.ra'uf domin hirar zumunci ,bahijja da basma suma suka wuce dakin da aka sauke su , anwar ,anas ,aisha da zarina kadai aka bari a falon , anas charaf ya tashi ya matso kusa da sahibar tasa ,ko kallo bai isheta ba ,ta tashi ,anwar ya miqe ya bi hanyar da zarina ta bi ........a hanyar kitchen suka hadu ..........ya ja hannunta ,suka fice suka nufi garden ,suna xuwa ,kawai sai ya rungumeta tare da sakin wani irin kuka mai ciwo 'zarina i cn xpress hw mch ur love means 2me ' bansan taya na fara sonki ,sonki abune da ya shigeni ba tare da nasani ,ina sonki ,i love u zarina ......ta janye jikinta ....ta juya mai baya ,tace anwar dole mu rungumi kaddara ,its too late 2cry ,biyayya kam ya zama dole ,soyayyarmu bata qare mu da komai ba ,saima ta shin hankali, anwar ina sonka ,gangar jikina za'a kaiwa anas amma zuciyata taka ce,ina sonka,akan ka nasan menene so , akan na fara sanin dadin so ,kuma akanka nasan zafin rabuwa da masoyi ,....zarina kin yarda mun rabu kenan ......ta dubeshi tayi murmushi mai ciwo.......idan so cuta ne ,.....hakuri magani ne......taja baya ta bar gun a guje ,tana mai zubda hawaye............duk abunda ya faru tsakaninsu yanxu , akan kunnen da idanun ........ANAS yafaru.... : KYAUTAR BUDURCI PART 7 Yau alhamis wato jajiberin daurin auren ANAS da ZARINA ,ANWAR da AISHA,, hankulan masoya biyu wato anwar da zarina ya kai matuqar tashi ,bbu walwala a tattare dasu , komai ciki karfin hali suke yi , hatta gyaran jiki da kunshi karfin hali kawai zarina tayi..............har dare yayi ,yau bata ga anwar ba ,hankalinta ya tashi ,ga wani matsanancin son da take ji yana taho mata har wuya ........yanxu haka ta kwance ta kurawa cieling ido .....yanxu gobe i war haka ,naxama matar aure,matar anas .mrs anas , ....ta fashe da wani irin kuka ....ji take kamar dama ta mutu ta huta ....... Anwar ba da kai zanyi rayuwa ba,ba kaine uban yayana ba,kaddara ta zaba min anas a matsayin mijin aurena ........ta dubi agogo karfe 12:30 na dare , ta sauko daga kan gado ,ta nufi kofar fita dakinta ta fito.....gdan tsit alamun kowa ya kwanta ......kawai sai ta nufi side din da anwar yake ,ta nufi dakinsa ,ta murda kofar ta ji ta a bude ta shiga ..........Ido biyo ta tarar da anwar ,idanunshi a kumbure ,wato shima yana cikin halin datake ......ya dubeta a razane , 'lafia ki ka zo min daki a tsohon darennan ' ta dubeshi .yaya anwar nazo muyi ,sallama ,nazo muyi bankwana g.obe xa'a zargamin igiyar auren anas......ya rintse ido ,yana mai jin yaji yaji a zuciyarsa.......... Shiru ya ziyarci gurin ....ta qarasa gabansa ta rusuna a gabanshi tana mai cewa 'yaya anwar naxo ne in yi maka KYAUTAR so , nazo in baka KYAUTA kafin mu rabu ,nazo inyi maka KYAUTA a wannan dare kafin a daura aurena gobe ,ba abunda mace take tutiya ta kai gdan miji kamar BUDURCINTA , BUDURCI shine abunda ko wanne ango zai so ya samu a gun amaryarsa, Yaya anwar ,BUDURCINA naka ne kai kadai ,baxan iya sallamawa ko wani namiji BUDURCINA ba ,kaine Namiji tilo da yakamata Ka mallaki BUDURCINA . kamar yadda zuciyata ta zama taka .......haka nakeson BUDURCINA ya zama naka ......yaya anwar na baka 'KYAUTAR BUDURCINA ...........(shin ana haka kuwa?).... : KYAUTAR BUDURCI : KYAUTAR BUDURCI PART 8 Anwar ya dubeta a firgice ,ya miqar da it tsaye ,yana girgizata 'zarina lafiarki kalau kuwa ,in mafarki kike ,ki farka, haba wacce irin KYAUTA ne wannan , zarina u dnt hv 2 do dis ,kafin in san cewa u love me deeply ba ,i wannan rashin tawakkali ne ,da rashin yadda da kaddara ,zarina plz kiyi hakuri mu bar maganar KYAUTAR nan ....... Zarina ta dubeshi da jajayen ido 'anwar ashe baka sona .ashe son da kake be kai so ba ,if u truly love me u better accept my GIFT 2 u , ...... Anwar ya dubeta 'in har aikata zina ,shine zai tabbatar miki da cewa ina sonki ,toh zarina naji na yadda bana sonki din ...... Ya juya mata baya ....... Anwar ka gwammace waninka ya rigaka kusantata ,ka yadda cewa anas shi yafi chanchanta da ya mallaki BUDURCINA ....... indai akan sonka ne ,anwar bana gani bana ji ..........da akan in mallakawa anas BUDURCINA gwara na rasa raina ....... A firgice anwar ya juyo 'zarina nafison karban BUDURCINKI cikin mutunci, a karka shin inuwar aure ..... Ta dubeshi tace 'kuma kaddara ta hana hakan ' saita fara cire kayanta .......har ya zamto daga ita sai fatar jikinta ........anwar ya rintse ido ,wani abu na mai yawo a jiki , tana hawaye tazo ta rungumeshi , kam kam ya riqeta , ya kaita kan gado.........cikin halin kuka da bege ,da zazzafar so .a wannan dare Anwar ya raba zarina da BUDURCINTA ....... PART 9 3:00am ...suka dawo hankalinsu ....zarina in banda kuka ba abunda take ,ga zafin first tym ,ga kuma tarin nadama duk da dai tasan masoyinta ta bawa kanta ,ba ta da asara ... Anwar ji yayi kamar an zare mah son zarina daga zuciyarshi .....fit! Soyayyar zarina 8a fita daga zuciyarshi........ Ya tashi ko kallonta baiyi ba ya fada toilet .......ita haka taja kafa ta fice ta nufi dakinta ...toilet ta nufa ta kimtsa kanta ......amma duk da haka tafiyar tata sai a hankali ......... Ranar juma'a da safe kowa ya hallara a dinning ...ana breakfast .......zarina da anwar sun kasa hada ido ,ita matsanancin kunyarsa take ,shi kuma haushi ,da kiyayyarta ne fal xuciyarsa ,ba ta da wani daraja a idanunsa,ta sashi ya aikata zina under d same roof dt he's livn wit his parent .......bayan an kamalla ,anas ya dubi iyayensa duka ukun wato Alh.ra'uf ,rabiu da ridwan .....ya rusunna yace yana da magana ......... Anas ya juye musu komai dangane da soyayyar zarina da anwar ,yace a gaskiya ban cancanti in auri zarina ba ,anwar ne ya kamata ya aureta ,sun dade suna son juna fada ne kawai basuyi ba ,amma abba ina neman alfarmar da a bawa anwar zarina ,nikuma ko bahijja da basma ne a zaba min daya daga cikinsu .......Alh.ra'uf ya numfasa yace 'daman kai kaganta kace kanaso ,tunda ka bar wa anwar ,da kai da shi duk dayane , sai a maida auren kanshi..........wani sanyin dadi ne ya ziyarchi zuciyar zarina tana mai hamdala ga rabbis samawati Budar bakin anwar sai cewa yayi ,tsakanina da zarina bbu wata soyayya hasashe ne dai irin na anas ........amma ni zabin aishar da kuka zaba min shine zabina abba .......don bazan boye muku ba aysha tafi zarina kwanta mini.......kuma abinda yayi zarina shiyayi aiisha......zarina ta kwalalo ido ......hmm wannan shine ta leqo ta koma (kunga laifinsa? Ni dai nace #GAME_OVER ) : KYAUTAR BUDURCI PART 10 alh.ra'uf ya sauke numfashi 'shikenan duk babu matsala,anas daman kai kace kanason zarina,tunda yanxu ka janye,toh anjima za'a daura auranka da basma,bahijja da zarina kuma Allah ya kawo muku mazaje,gaba dayanku duk daya kuke a guna,bbu tilastawa' ,a haka aka gama cin abinci aka watse da niyyar bayan sallar juma'a a daura aurensu anwar,zarina jiki a sanyaye taja kafafunta ta shige daki,ta rufo kofar ,idanunta suka fara zubar hawaye,tana mai danasanin abinda ta aikata a daren jiya,oh ynzu haka anwar zai mini,oh Allah ina mai kunyar daga hannayena in ro'keka gafara bisa abinda na aikata dalilin son zuciya da rashin tawakkali,Allah na tuba ka yafemin ,ka kawo min d'auki ga wannan halin da na jefa kaina a ciki,a daidai lokacin haj.lubna ta shigo,ta nemi gu kusa da zarina ta zauna ,a sanyaye tace 'yanayinki kad'ai ya nunawa cewa kamar an miki fyad'e zarina','dama fyad'e aka min da da sauki wlh' ,zarina take fad'i a zuciyarta,idanunta na zubda hawaye ,ta labartawa haj.lubna komai dangane da daren jiya,hannu akan kirji tare da kwalalo idanuwa,haj.lubna ta maimaita kalmar 'KYAUTAR BUDURCI' a firgice. PART 11 hannu biyu haj.lubna tasa tana jibgar zarina cikin 'kunar rai,tana had'a kanta da katako gado,tare da zabga mata zafafan mari,zarina ko motsawa batayi ba,sai da haj.lubna ta gaji dan kanta ta kyaleta,tana cewa 'tir zarina,tir wlh,BUDURCIN dungurgum kika d'auka ki ka bawa saurayi kyauta,wai ke gaki 'yar dadi soyayya ko,wlh kin tabka kuskure babba,kuma ni banga laifinsa ba,yayi min daidai,toh mezaiyi dake bayan hakan ta faru,mace anyi auran ,ta kai budurcinta gidan miji ,ya ta 'kare da wulakancin d'a namiji,ina ga toh ka d'au budurcin ka bashi kyauta,sai kuma abinda hali yayi,da yake Allah ba azzalumin bawansa bane,anas bashi da hakkinki ,hakan yasa aurenki dashi ya warware cikin sauki,ya kuma musanya masa da wata,da kinyi hakuri ,da yau kin zama matar anwar ,da kinyi tawakkali kin miqa lamuranki ga Allah, da yau kin ga sakayyar mai cike da khairan,amma ina! Sai kikayi gaban kanki ,ki ka dau budurcin kacokam kika bashi kyauta,toh ynzu wa gari ya waya,baki da tsuntsu ,ba ki da tarko,kin rasa anwar,kin rasa anas,kin rasa budurci,asara uku kenan,shi kuwa gashi can za'a d'aura auransa ya kuma amsar wani budurcin,bayan wanda aka bashi kyauta,zarina kinyi kuskure mai mugun muni',zarina kuka take kawai mai cin rai, tana mai dana sani wanda hausawa sukace 'keyace,haj.lubna ta fice ta barta anan..[kunga laifin haj.lubna?] : KYAUTAR BUDURCI PART END karshe' Bayan shekara 1 anas shi da matarsa basma sun wuce asia domin a can yake aiki anwar da aisha suna zamansu lfy ,ya kamalla bautar kasa,yana aiki a kano.. Zarina ta dawo so silent,ta mugun yin sanyi,cAs ta daina xuwa,ta rungumi zaman gda da zaman daki,ibada da istigifari kawai take,ta zamto abar tausayi ,har haj.lubna da kanta ta sauko daga fushin da tayi da ita,alh.rauf ya tmby lfy,amma kawai sunce masa yanayin rayuwane ya maida zarina haka,shima ya xuba mata ido.. Wata rana anwar yaje misau,mahaifinsa mal.ridwan ya dubeshi yace 'ina umartarka da kaje ka nemi auran zarina,ko da baka sonta,ita tana sonka,domin naga hakan idanunta ,kawaici kawai tayi a ranar da anas ya fasa aurenta kai kuma ka nuna baka ra'ayinta ',anwar bai da za6i illa ya bi umarnin mahaifinsa,aka d'aura auren anwar da zarina ,ta tare ,tsakaninta da aisha bbu matsala,amma a idon anwar aisha ta fita daraja,saboda ya samu budurcinta a karkashin inuwar aure ,sa6anin zarina data bashi KYAUTAR BUDURCINTA ,ita kanta zarina tasan KYAUTAR BUDURCI bai kareta da komai ba ,domin a dalilin KYAUTAR BUDURCI ta rasa SO,MUTUNCI,DARAJA,KIMA,a gun anwar ,ita kuma aisha a dalilin ta kai BuDURCINTA dakin mijin aurenta ta samu SO,DARAJA,MUTUN CI,KIMA, a gun anwar...sai dai muce Allah ya bawa zarina da anwar zaman lafiya(tammat) *** a nan nakawo karshen gajeren labarin KYAUTAR BUDURCI ,gareku mata dan ALLAH ku kiyaye budurcinku,domin budurcinku shine martabarku,duk wuya duk rintsi,duk wulakacin d'a namiji ,zaifi ki kai masa budurcinki bayan ya biya sadakinki kuma an shaida an shafa fatiha,amma KYAUTAR BUDURCI babba asara ce ga d'iya mace ko da kuwa hakan na nufin faranta ran wanda aka bawa Kyautar naku har abada (c)Abdul'aziz Ililie Isma'il : KYAUTAR BUDURCI AREWAPRESS1.com.ng
0 Comments:
Post a Comment