Friday, 14 September 2018




Abdullahi shehu Dan wasan Super Eagles zai yi wa Sakkwatawa kyauta kan kano Pillars

Home Abdullahi shehu Dan wasan Super Eagles zai yi wa Sakkwatawa kyauta kan kano Pillars

Anonymous

Ku Tura A Social Media

Dan wasan bayan tawagar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles, Shehu Abdullahi ya yi alkawarin bai wa kungiyar kwallon kafa ta Sokoto United kyautar kudi idan suka ci Kano Pillars.

A wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Abdullahi ya yi alkawarin bai wa kulob din na Sokoto naira 100,000 kan kowace kwallon da ya ci idan ya samu nasara a kan kungiyar Kano Pillars.

Sokoto United za ta kara da Kano Pillars a wani wasa na gasar Aieto Cup wadda ake ce wa gasar kalubale.

Dan wasan, wanda a yanzu haka yana taka leda a kungiyar Bursaspor ta Turkiyya, ya ce ya dauki wannan matakin ne domin nuna goyon bayansa ga tsohon kulob dinsa.

Duk da cewa Abdullahi ya taba buga wa Kano Pillars wasa, dan wasan ya ce ya yi sakon bidiyon ne ga hukumar gudanarwa da kuma 'yan wasan kungiyar Sokoto United.

Ya ce "ga duk wani kwallon da kuka ci kano Pillars tare da nasara, zan ba ku naira 100,000.

"Idan kuka ci kwallo biyu za ku samu 200,000, idan kuka ci uku za ku samu 300,000. Idan za ku iya cin biyar zuwa goma, zan ba ku kudinsu."

Daga nan sai ya yi wa Sokoto United din fatan alkhairi a wasan.

Dan wasan dai ya yi wasa a Sokoto United da Kano Pillars da Qasida FC na Kuwait kafin ya koma taka leda a Turai.

Sokoto United dai ta fitar da MFM, da ke buga gasar Firimiyar Najeriya, a gasar kafin wannan karawar da za ta yi da Kano Pillars.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: