Shahararren jarumin fina-finan Hausa ta
Kannywood, Adam A Zango, ya nemi gafarar
jarumi Ali Nuhu a wani sakon da ya wallafa a
shafinsa na Instagram.
Sakon mai dauke da wani hoton da ya nuna
Zango ya durkusa kuma Ali na zaune bisa kujera,
ya zo ne kwanaki bayan Zangon ya wallafa wasu
hotunansa da Ali a Instagram bayan sun kwashe
kwanaki suna "gaba".
Sakon Adam Zangon ya ce "tuba nake sarki
gwiwowina a kasa".
Tuni dai magoya bayan jarumin suka fara tofa
albarkacin bakinsu kan hoton da Zangon ya
wallafa a shafinsa na Instagram.
0 Comments:
Post a Comment