Kasashen Najeriya da Syria da Afghanistan, da
Iraqi da kuma Yemen su ne a sahun gaba a jerin
kasashen da aka fi samun kashe-kashen
al'umma sanadiyyar rikice-rikice a cikin shekara
biyar da suka gabata.
Hakan dai na kunshe ne a cikin wani rahoto na
cibiyar bincike ta Brookings institute da ke
Amurka.
Rahoton ya sanya Najeriya a matsayi na hudu,
da yawan mutane wadanda aka kashe da suka
kai Dubu ashirin da hudu da casa'in da bakwai
(20,497).
A baya-bayan nan dai Najeriya ta fuskanci karin
hare-hare da ake zargin kungiyar Boko Haram da
kai wa, da fadan da ake bayyanawa a matsayin
na manoma da makiyaya.
Barista Audu Bulama Bukarti, malami ne a
jami'ar Bayero da ke Kano, kuma manazarci a
gidauniyar Tony Blair foundation da ke birnin
Landan ya ce rahoton ya na yi wa Majalisar
Dinkin Duniya hannun ka mai sanda ne.
Kan kasashen da ya kamata su maida hankali a
kai dan ceto al'umarsu, maimakon wasu
kasashen na daban da suke gudanar da aiki.
Bukarti ya kara da cewa, ita kan ta gwamnatin
Najeriya babban tashin hankali ne a gare ta a ce
cikin shekara biyar an kashe sama da mutane
20,000 a kasar, inda nan ma ya kamata ta zage
damtse dan ganin ta bai wa 'yan kasar kariyar da
ta dace.
Rikicin Boko Haram, da na barayin shanu, na
daga cikin matsalolin da Najeriya ke fama da su
a dan tsakanin nan wanda kuma ke janyo
mutuwar fararen hula da asarar dukiya. kukasan ce da mu akodayau she wajjen ziyar tar www.Arews.com.ng
Monday, 24 September 2018
Author: Anonymous verified_user
RELATED STORIES
Lagos taci Ado Domin Bikin Kirsimeti click here👇🏻Duk shekara birnin Lagos na Najeriya na shan ado
Man dies while trying to save girl, 13, from drowning at sea A 29-year-old man has died, while two otherTop newspeople have been transported to hospital
ADAM A ZANGO YANEMI GAFARAR ALI NUHUShahararren jarumin fina-finan Hausa taKannywood,
Yan sa-kai na 'kashe mutane a kasuwannin Zamfara'Yan sa-kai na 'kashe mutane a kasuwannin Zamfara'
About 10,000 light years away from Earth, a black hole is engaged in a stellar feastAbout 10,000 light years away from Earth, ablack
List of Schools that offer Medicine and Surgery under the Faculty of Medical, Pharmaceutical & Health Sciences in Nigeria.Medicine and Surgery - Faculty of Medical, Pharma
0 Comments:
Post a Comment