Tuesday, 25 September 2018




Kun san mutumin da ke son ya zama wanda ya fara zuwa shakatawa a duniyar wata?

Home Kun san mutumin da ke son ya zama wanda ya fara zuwa shakatawa a duniyar wata?

Anonymous

Ku Tura A Social Media
Yusaku Maezawa hamshakin mai kudi ne na
kasar Japan da aka fara sani a matsayinsa na
mai kada ganga a wata kungiyar mawaka.
Daga baya ya samu kudi a harkar sayar da kayan
sakawa ta intanet, kuma an san shi a wajen
Japan ta hanyar kashe miliyoyin daloli a wuraren
baje-kolin zane-zane da ke cike da tarihi.
A halin yanzu dai burin Mista Maezawa ya dara
zama kawai a duniyar 'yan Adam.
Yana da burin zama fasinja farin fula na farko da
zai fara tashi zuwa duniyar wata, a matsayin
wani bangare na wani shiri tare da kamfanin Elon
Musk, SpaceX.
Attajirin na Japan yana son ya yi tafiya da wasu
masu yin zane-zane, a tafiyar da aka saka ran
cewar za a yi a shekarar 2023.
Kawo yanzu dai Mista Maezawa, mai shekara 42,
bai bayyana adadin kudin da ya biya domin
tafiyar ba, lamarin da ya hada hamshakan masu
kudi wadanda ba su damu da kasancewa a
bainar jama'a ba.
Dan kasuwar na Japan ya fara sayar da tsaffin
faya-fayen CD da wakoki a shekarar 1998 ta
wani kamfanin da ya samar mai suna Start
Today.
Harkar tasa ta ciniki ta hanyar wasika ta koma
kan intanet a karshen karnin da ya gabata ya
kuma kara kayayyakin sakawa cikin abubuwan da
yaka sayarwa.
A farkon wannan shekarar, ya sanar da jaridar
Japan Times cewar "Na kasance shugaban
kamfanina a lokacin da nake yawo cikin kasar da
kungiyar kade-kadena.
Da ya zama wani abin da ba zai yiwu ba in hada
harkokin biyu, na zabi kamfanina - a wancan
lokacin ina mai shekara 25 zuwa 26."
Ya kaddamar da kamfanin sayar da tufafin
zamani ta intanet Zozotown a shekarar 2004,
kuma ya zama biloniya a lokacin da yake da
shekara 30 da 'yan kai.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: