An soki jaruman fim din Hausa Akan Rashin Taimakawa Juna: Ali Nuhu ya Mayar Da Martani
Ma'aikaciyar tashar talabijin ta Arewa24, kuma marubuciya, Fauziyya D. Sulaiman ta fito ta dandalinta na sada zumunta ta nemawa tauraron fina-finan Hausa, Baba Karkuzu taimako akan biyan kudin haya, daga baya Fauziyya ta fito ta bayyana cewa, Ali Nuhu ya biya kudin, saidai wannan batu ya bar baya da kura.
Wasu sun tofa albarkacin bakunansu akan wannan lamari inda suke ganin cewa, akwai abin mamaki ganin mutane irin su karkuzu duk da shekarun da suka shafe a wannan masana'anta amma biyan kudin haya yana musu wuya.
Wani yace, gaskiya toh Allah ya wadai da Kannywood, da suke barin manyansu na fama da irin wannan matsalar, Allah shi kyauta.
Ali Nuhu ya mayarmai da amsar cewa, kana da damar fadin ra'ayinka amma ya kamata kasan kowa ya kamata yayi tanadi tun kuruciyarshi.
Wani ma ya kara fadin cewar, nasha na yi tsammanin kuna da tanadin da kukewa irin wadannan mutane?
Shima Alin ya bashi amsar cewa, Me kake nufi? Wannan masana'antace da ya kamata ace kowa yana da ma'aikata/masu gudanarwa da zasu rika bashi shawara kan yanda zai sarrafa dukiyarshi.
0 Comments:
Post a Comment