Babban na hannun-daman Kwankwaso, Farfesa Hafiz, ya fita daga PDP
LABARAI DAGA 24BLOG
Tsohon mataimakin gwamnan Kano Farfesa Hafiz Abubakar ya fice daga jam'iyyar PDP mai hamayya a jihar.
Farfesa Abubakar babban na hannun-daman tsohon gwamnan jihar Rabi'u Musa Kwankwaso ne.
Wasu majiyoyi sun shaida wa BBC cewa ranar Laraba zai bayyana dalilansa na ficewa daga jam'iyyar.
Sai dai a wata wasika da ya aike wa shugaban jam'iyyar na mazabarsa ta Mandawari, Farfesa Abubakar, ya ce ya fita daga jam'iyyar ne domin radin kansa.
A watan Agusta ya sauka daga kujerar mataimakin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje sannan ya fice daga jam'iyyar APC ya koma PDP inda uban gidansa, Sanata Kwankwaso yake.
A wancan lokacin, Farfesa Hafiz Abubakar ya ce ya fita daga APC ne saboda gwamnan jihar yana barazana ga rayuwarsa.
Ganduje yana gana min azaba - Mataimakin Gwamnan Kano
Shin Ganduje zai rantse da Alkur'ani?
Me ya sa Kwankwaso ya tsayar da 'surukinsa' takarar gwamna?
Sai dai daga bisani ya koma PDP inda ya nemi tsayawa takarar gwamnan jihar a inuwar jam'iyyar.
Zabukan fitar da gwanin da aka yi a jam'iyyar reshen jihar Kano sun bar baya da kura sakamakon tsayar da Malam Abba Yusuf - surukin Sanata Kwankwaso - a matsayin mutumin da zai yi takarar gwamna a PDP.
Rahotanni sun ce wannan mataki bai yi wa wasu jiga-jigan jam'iyyar a jihar dadi ba, cikinsu har da Farfesa Abubakar, wanda ya yi tsammani shi za a tsayar a matsayin dan takara.
Fitar sa daga jam'iyyar ta PDP ka iya kawo mata matsala a zabukan 2019 musamman saboda da matsayinsa na mutumin da a baya ba ya jayayya ga duk matakin da tsohon gwamnan jihar ya dauka.
Wednesday, 31 October 2018
Author: Anonymous verified_user
RELATED STORIES
JAMB: 2019 UTME ƙare, 'yan takara ku shirya don fara duba sakamakon.JAMB: 2019 UTME ƙare, 'yan takara ku shirya don f
An Kama Mutum 50 Kan Rikicin Siyasar Jihar KanoRundunar 'yan sanda ta jihar Kano a Najeriya ta c
ASUU Ta Janye Dogon Yajin Aikin Da Ta Shiga Tsawon Wata Uku Kungiyar Malaman Jami'o'i Nijeriya ASUU ta janye
Kaddamar da: Ayyukan IGP Adamu ya umarce su su rarraba FSARSKaddamar da: Ayyukan IGP Adamu ya umarce su su ra
El-CLASSICO: Dan Madrid Ya Kashe Dan Barcelona a Birnin KanoWani matashi a birnin Kano ya burma wa abokin sa
House of Reps ya ci gaba da karantawa na biyu na
0 Comments:
Post a Comment