Domin taimaka wa dalibai masu nazarin harshen hausa, da kuma masu so rubutunsu ya yi ma'ana da saukin karatu, ba tare da mai karatu ya canja wa rubutun nasu ma'ana ba.
DARASI NA BIYU.
Baƙin Alhamza (‘)
Na san wasu za su yi mamakin ganin na kira wannan alama da baƙi. To haka abin yake. Ana kiran sa da “Hamza” ko “Alhamza.”
Shi wannan baƙi ana rubuta shi ne yayin da ya zo a tsakiyar kalma. Ba a rubuta shi a farkon kalma, sai dai ana ƙaddara samuwarsa, don shi ne baƙi ga wasalin da a zahiri za a ga kalmar ta fara da shi, domin babu wata kalma da ke farawa da wasali a Hausa. Ba ya kuma zuwa a ƙarshen kalma.
Misali,
A farkon kalma:
‘amfani, ‘aure, ‘ido, ‘unguwa, ‘ofis, ds.
A tsakiyar kalma:7
Ma’auni, Sa’idu, shu’umi, nau’o’i, ds.
Baƙaƙen /w/ da /y/
Duk da kasancewar waɗannan sautuka biyu baƙaƙe ne, akan yi amfani da su a matsayin wasula don nuna faɗuwar wasali. Dalili ke nan akan kira kowannensu da “Ƙanen Wasali.”
Ba a yin ɗauri da su sai idan baƙin gaɓar da ke biye irinsu ne.
Misali:
taiki ba tayki ba
ƙauye ba ƙawye ba
amma:
bayyana ba baiyana ba
gayyata ba gaiyata ba
yawwa ba yauwa ba
tsawwala ba tsauwala ba
Sautin /ph/
Sautin /p/ dai na cikin sautukan Turanci da ba a amfani da su a Hausa, ballantana a sami goya masa wani sautin. Don haka amfani da irin wannan goyo wajen rubuta wasu sunaye kuskure ne. Misali:
Musɗafa ko Mustafa ba Mustapha ba
Halifa ba Halipha ba
Ɗaurin Baƙin /m/ da /n/
Wannan ƙa’ida ta shafi zaɓi ne tsakanin baƙin /m/ ko /n/ dangane da ɗauri yayin da suka zo a tsakiyar kalma.
Ana yin ɗauri da /m/ ba /n/ ba a tsakiyar kalma, idan baƙin da ke biye ya kasance ɗaya daga cikin wasu baƙaƙe huɗu da ake leɓantawa, wato ake danƙe baki yayin furta su ya biyo baya. Baƙaƙen su ne /b/, /ɓ/, /f/ da /m/.
Misali:
tambari ba tanbari ba
rumbu ba runbu ba
hamɓare ba hanɓare ba
tumɓuke ba tunɓuke ba
tumfafiya ba tunfafiya ba
shimfiɗa ba shinfiɗa ba
hammata ba hanmata ba
gammo ba ganmo ba
Idan kuma ɗaurin ya zo a ƙarshen kalma ne, to da /n/ za a yi, ba da /m/ ba, ko da kuwa baƙin farko na kalmar da ke biye ya kasance ɗayan /b/, /ɓ/, /f/ ko /m/ ne.
Misali:
ɗan birni ba ɗam birni ba
ɗakin baƙi ba ɗakim baƙi ba
yawan magana ba yawam magana ba
ramin ɓera ba ramim ɓera ba
‘yan fashi ba ‘yam fashi ba
Kalmomin amsa-kama masu ƙarewa da /m/, ba a sauya /m/ ɗin da /n/.
Misali:
jingim ba jingin ba
sukutum ba sukutun ba
tsundum ba tsundun ba
Haka ma:
kullum ba kullun ba
mutum ɗaya ba mutun ɗaya ba
Malam Ali ba Malan Ali ba.
Wannan wani sabon darasi ne da Waziri Aku tare da haɗin gwiwar Shafin Muryar Hausa24 su ka ɗauki nauyin kawowa 'yan uwa ɗalibai masu yin nazarin harshen Hausa da kuma masu son koyon ƙa'idojin rubutun harshen Hausa domin rubutunsu ya yi ma'ana da sauƙin karatu, ba tare da mai karatu ya canja wa rubutun nasu ma'ana ba.
A lura da haƙƙin mallaka wajen kwafin ɗin rubutu, darasin zai rika zuwa muku duk ranar Juma'a, daidai wannan lokaci, tare da taimakon Malam Nasir G. Ahmad.
KARANTA KAJI: MU KOYI RUBUTUN HAUSA DA KA'IDOJINSA KASHI NA FARKO
Za mu ci gaba a sati mai zuwa Ranar Juma'a Insha Allah, Idan akwai mai tambaya a kan wannan darasi na yau sai a tura tambaya zuwa muryarhausa24@gmail.com mungode .
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu
Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke
Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.
DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki
Mungode
Source: www.MuryarHausa24.com.ng
0 Comments:
Post a Comment