Zabukan fitar da gwanin 'yan takarar shugaban
kasa a Najeriya na nuna cewa takarar yanzu ta
koma tsakanin shugaba mai ci, Muhammadu
Buhari na Jam'iyyar APC da tsohon mataimakin
shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar na
jam'iyyar PDP.
Kowannensu yana da karfi irin nasa. Shugaba
Buhari mutum ne wanda kimarsa ta zama jarinsa
a siyasar Najeriya kamar yadda shi kuma Alhaji
Atiku Abuakar ke daukar wayewarsa a matsayin
wani jari da zai kai shi ga ci.
Ya rage wa 'yan Najeriya su zabi daya daga cikin
wadannan mutane biyu da zai zama shugaban
kasar idan har an yi zaben gaskiya da adalci.
Ko shakka babu, Shugaba Buhari ya nuna shi
mutum ne mai kyawun hali, wanda ba ya karbar
cin hanci, kuma ba ya bayarwa, ba ya goyon
bayan a karba, ko a bayar, kuma yana nisantar
aikata abin kunya.
Ya tabbatar wa 'yan kasar cewa shi mutum ne
da zai iya rike amanarsu, al'amarin da ya kawo
masa rashin jituwa tsakaninsa da wasu abokansa
da 'yan uwa da masoya.
Ina Buhari yake da rauni?
Amma masu nazarin harkokin siyasar kasar suna
ganin yana da wani rauni a matsayinsa na
shugaba.
Ana zarginsa da yin saka-saka da harkokin mulki,
da rashin daukar mataki kan mukarraban
gwamnatinsa da ke saba wa umurninsa.
An ce ya sakar wa wasu 'yan barandarsa
ragamar mulkin kasar wanda ya janyo wasu
manyan kura-kurai da bai kamata su faru ba.
Haka kuma, wasu na ganin cewa tsarin tattalin
arzikin da gwamnatinsa ta kawo yana barazana
ga rayuwar ma'aikata masu matsakaicin albashi,
da jefa talakawa cikin mummunan talauci.
Ana yi wa shugaban kallon mutumin da ya zo
don gyara barnar da ya ce jam'iyyar PDP ta yi a
cikin shekaru 16 da ta yi tana mulkin kasar.
Ya kudiri niyyar gina abubawan more rayuwa
kamar su tinutan mota da titunan jirgin kasa da
filayen jiragen sama da makarantu da asibitoci
da samar da wutar lantarki don dawo wa kasar
da martabarta da tattalin arzikinta da ya rushe.
Kwarewar Atiku
Shi kuwa Atiku Abubakar, mutum ne da ke da
wayewa kan harkokin kasuwanci a kasashen
Amurka da yankin Turai da Asiya da Gabas Mai
Nisa.
Ana yi masa ganin mutum ne da ya yi fice wajen
tsamo mutane masu basira a fannoni daban-
daban, duk da cewa shi ba irin su ba ne.
0 Comments:
Post a Comment