Tuesday, 30 October 2018




SHARRI YAN SANDA SUKAYI MANA CEWAR YAN SHI'A

Home › › SHARRI YAN SANDA SUKAYI MANA CEWAR YAN SHI'A

Anonymous

Ku Tura A Social Media
Mabiya Shi'a sun musanta zargin da jami'an tsaro ke musu na cewa sun koma wata motar 'yan sanda yau a yankin Wuse 2, bayan sun tashi daga wani gangami da suka shirya a garin Abuja.
Wakilin Shaik Zakzaky na garin Kano Dakta Sunusi Abdulkadir yana daga cikin wadanda suka jagoranci gangamin ya bayyanawa manema labarai yau cewa ba su da masaniya da wannan aikin yana me cewa “mune aka kashe aka kama wasun mu aka ji mana raunuka bayan mun fito bayyana kiranmu akan a sake mana Malaminmu.
Ya kara dacewa “muna masu nisanta kanmu da wannan aiki kuma muna zargin jami'an tsaro sun yi haka ne domin gogawa wannan harkar kashin kaji”

Share this


Author: verified_user

0 Comments: