Jami'ar El-razi dake kasar Sudan ta kori daliban nan 'yan Jihar Kano kuma 'ya'yan talakawa da Gwamnatin Dr Rabi'u Musa Kwankwaso ta tura su Jami'ar domin su karo karatu.
Jami'ar ta dauki wannan mataki ne sakamakon kin cigaba da daukar nauyin Daliban da Gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta yi, duk wani kokari da jami'ar ta yi na ganin daliban sun ci gaba da daukar darussa abun ya ci tura saboda Gwamnatin ta ki cewa komai game da tulin wasiku da Jami'ar ta turawa Gwamnatin Kano akan lamarin.
Yanzu haka dai Daliban suna cikin wani mummunan yanayi kasancewar hatta kudin abinci ma ba su da shi ballantana kudin jirgin da za su biya su dawo gida ga kuma iyayensu Ttalakawa.
0 Comments:
Post a Comment