Thursday 29 November 2018




bayan halartar taro a kasar Chadi Bidiyon Ganduje: 'Yan majalisun tarayyar APC na jihar Kano sun fadi ra'ayoyinsu

Home bayan halartar taro a kasar Chadi Bidiyon Ganduje: 'Yan majalisun tarayyar APC na jihar Kano sun fadi ra'ayoyinsu

Anonymous

Ku Tura A Social Media
[post by samaila umar lameedo]
bayan halartar taro a kasar Chadi
Bidiyon Ganduje: 'Yan majalisun tarayyar APC na jihar Kano sun fadi ra'ayoyinsu

LABARAI DAGA 24BLOG
- Sanatoci da 'yan majalisar tarayya na jam'iyyar APC na jihar Kano sun ce har yanzu sun tare da gwamna Abdullahi Ganduje da Shugaba Muhammadu Buhari
- 'Yan majalisan sun ce ba za suyi sharhi a kan bidiyon da aka fitar na gwamnan yana karbar daloli da ke zargin rashawa ce domin lamarin na kotu
- Sai dai 'yan majalisan sun ce sharri 'yan adawa suka yiwa gwamna Ganduje kuma sunyi imanin kotu za ta wanke shi
'Yan majalisar wakilai na tarayya na APC sun ki cewa uffan a kan fayafayen bidiyon da aka saki da ke nuna Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na karbar daloili daga hannun 'yan kwangila da ake zargin rashawa ce.
Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan majalisar na jam'iyyar APC guda bakwai sun hadu ne a harabar majalisar tarayyar domin jadada goyon bayansu ga gwamnan jihar na Kano.
Sai dai bayan sun kammala karanto jawabinsu inda suka jinjina wa gwamnan kan nasarorin da ya samu tun kama aiki a shekarar 2015, yan jarida sun jefa musu tambayoyi.
Bidiyon Ganduje: 'Yan majalisun tarayyar APC na jihar Kano sun fadi ra'ayoyinsu
Sanata Kabiru Gaya, wadda shine ciyaman din na yan majalisar na jihar Kano ne ya karanta jawabin yabo ga Ganduje.
A yayin da 'yan jarida suka tambayi ra'ayinsu kan fayafayen bidiyon, yan majalisar sun ki amsa tambayar inda suka ce har yanzu lamarin yana gaban kuliya.
Wanda ya fara amsa tambayar shine bulaliyar majalisar, Ado Doguwa, wadda shima jagora ne a kungiyar na 'yan majalisar Kano. Ya ce, "Ba za mu iya yin wani tsokaci a kan batun ba. Har yanzu batun na gaban kotu saboda haka yin magana a yanzu ya zama katsalandan cikin lamarin."
Shima, Sanata Jibrin Barau ya ce: "Kun san cewa wannan batun yana kotu amma muna kyautata zaton gwamnan zaiyi nasara a kotun da izinin Allah."
Yan majalisar na tarayya sun kuma zargi jam'iyyar adawa da kirkirar sharri domin bata wa gwamna Ganduje suna.
"Mu har yanzu muna tare da gwamnan mu da kuma shugaban kasa, kuma muna nan kan bakar mu da bawa shugaban kasa kuri'u miliyan biyar a babban zaben 2019."

Share this


Author: verified_user

0 Comments: