Thursday 29 November 2018




Bayanin shugaban kasar nigeria gameda kasashen tafkin chadi

Home Bayanin shugaban kasar nigeria gameda kasashen tafkin chadi

Anonymous

Ku Tura A Social Media

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi kira ga shugabannin kasashen yankin Tafkin Chadi da su kara hada kai domin magance matsalar tsaro a yankin.

Shugaban yana magana ne a birnin Ndjamena na kasar Chadi a lokacin wani taro na musamman tsakanin shugabannin kasashen da ke cikin hukumar mai suna Lake Chad Basin Commission.

An kira taron ne sakamakon karuwar hare-hare da ake samu a yankin a 'yan watannin nan, kuma shugaban na Najeriya ya nemi takwarorinsa daga Chadi da Nijar da Jamhuriyar Kamaru da su kara kaimi wajen dakile mayaka, musamman na kungiyar Boko Haram.
Advertisement

    Hotunan ziyarar da Buhari ya kai Maiduguri
    Buhari ya kira taron shugabannin yankin Tafkin Chadi kan Boko Haram

"A wannan lokaci ne muka fi bukatar daukar matakai na gaggawa," inji Shugaba Buhari.

Ya kuma bayyana cewa yankin ya fuskanci karuwar hare-hare da suka janyo tabarbarewar tsaro, musamman ma a kan sansanonin sojoji daga kungiyar Boko Haram wadanda suka hada da satar mutane.
Hakkin mallakar hoto MUHAMMADU BUHARI
Image caption Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar da Shugaba Buhari da Shugaba Idris Deby na Chadi da kuma Firai ministan Kamaru Philemon Yang

Shugaban ya kuma nemi shugabannin kasashen da suka halarci taron da su tashi tsaye wajen samar da ruwa ga tafkin na Chadi daga yankin Congo.

Shugaba Buhari ne ke jagorantar taron koli na shugabannin kasashen yankin tafkin na Chadi.
Hakkin mallakar hoto MUHAMMADU BUHARI
Image caption Daga dama: Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar da Shugaba Idris Deby na Chadi da kuma Shugaba Buhari

Shugabannin da suka halarci taron sun hada da Shugaba Idris Deby Itno na Chadi da Shugaba Mahamadou Issoufou Jamhuriyar Nijar da kuma Firai ministan Jamhuriyar Kamaru Philemon Yang, wanda ya wakilci Shugaba Paul Biya.

A sanarwar bayan taron da shugabannin suka fitar, sun jaddada cewa za su ci gaba da hada kai domin magance dukkan matsalolin ta'addanci da masu aikata manyan laifuka, har sai zaman lafiya ya dawo a yankin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: