Friday 30 November 2018




CAF ta kwace gasar kwallon kafa daga wurin Kamaru

Home CAF ta kwace gasar kwallon kafa daga wurin Kamaru

Anonymous

Ku Tura A Social Media
[post by samaila umar lameedo]
CAF ta kwace gasar kwallon kafa daga wurin Kamaru

LABARAI DAGA 24BLOG
Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka, CAF ta kwace damar da ta ba Kamaru ta daukar nauyin gasar cin kofin Afirka.
Hukumar ta ce ta dauki wannan matakin ne saboda yadda ake ta samun jinkiri wajen kammala ayyuka a filayen wasan da za a yi amfani da su a lokacin gasar da ake sa ran farawa a watan Yunin badi.
Jami'an hukumar ne suka yanke wannan hukuncin bayan wani taro da suka yi a Ghana a yau Jumma'a. An shafe fiye da sa'a goma ana taron.
Shugaban hukumar, Ahmad Ahmad ya ce za su cigaba da aikin samo "wata kasar da za ta karbi bakuncin kasashen da za su halarci wannan gasar nan da karshen shekarar nan."
Super Falcons ta tsallake zuwa wasan karshe
Wanda ya kirkiri rigar kwallon Brazil ya rasu
Gasar ta badi za ta kasance ta farko da aka taba gudanar da ita a watannin Yuni zuwa Yuli, kuma za a fadada yawan kasashe masu halarta daga 16 zuwa 24.
A bara ne Ahmad Ahmad ya ce sai Kamaru ta "tabbatar wa Kungiyar cewa za ta iya daukar nauyin wannan gasar" kafin a amince mata ta cigaba da shirye-shiryen da take yi.
Amma a watan Agusta shugaban kwamitin gudanar da gasar, Amaju Pinnick yace "Babu wanda zai kwace gasar a hannun Kamaru".
Ana ganin Maroko ce za ta karbi ragamar gudanar da wannan gasar kwallon kafa mafi muhimmanci a nahiyar Afirka, bayan da aka ce kasar Kenya ma ba za ta iya daukar nauyin gasar ba.
A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter hukumar ta CAF ta ce nan gaba kadan za ta yi karin bayani kan wannan mataki.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: