Majalisar ministoci a karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osibanjo ta amince da rage kudin Jarrabawar kammala sakandare ta NECO da kuma Jarrabawar shiga Jami'a ta JAMB.
Da yake karin haske kan zaman majalisar, Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya ce, daga yanzu duk dalibin da zai zana Jarrabawar NECO zai biya Naira dubu 9, 850 a maimakon Naira dubu 11,350 yayin da wadanda za su zana Jarrabawar shiga jami'a ( JAMB) za su biya Naira 3,500 a maimakon Naira 5,000.
0 Comments:
Post a Comment