Friday 30 November 2018




Jihar Zamfara za ta gurfanar da sarakunan gargajiya 7 saboda hada kai da 'yan bindiga

Home Jihar Zamfara za ta gurfanar da sarakunan gargajiya 7 saboda hada kai da 'yan bindiga

Anonymous

Ku Tura A Social Media
[post by samaila umar lameedo]
Jihar Zamfara za ta gurfanar da sarakunan gargajiya 7 saboda hada kai da 'yan bindiga

LABARAI DAGA 24BLOG
Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce nan ba da dadewa ba za ta gurfanar da wasu masu sarautun gargajiya bakwai a jihar saboda samunsu da hada kai da 'yan bindiga da ke kashe mutane.
Kwamishinan kananan hukumomi da sarautun gargajiya, Bello Dankande ne ya bayar da wannan sanarwar yayin da ya ke jawabi ga manema labarai a Gusau.
Ya ce wadanda za a gurfanar a kotun sun hada da hakimin Ruwan Gora, Isa Balarabe, hakimin Ruwan Rana, Altine Magaji da hakimin Ruwan Jema, Mohammed Sani.
Jihar Zamfara za ta gurfanar da sarakunan gargajiya 7 saboda hada kai da 'yan bindiga
Saura sun hada da dagacin Gurbin Bore; Marafa Zubairu, dagacin Baichin Birane; Danjeka Gyado, dagacin Gyado; da Hassan Mohammed, dagacin Tungar Dutsi.
Kwamishinan ya ce an samu sarakunan da laifin bawa 'yan bindigan mafaka tare da basu bayyanan sirri a kan shirye-shiryen hukumomin tsaro da kuma belin wasu daga cikinsu da 'yan sanda suka kama.
Ya yi bayanin cewa sashi na 15 (1,2 & 3) ya bawa gwamnan ikon tsige sarakunan daga kujerunsu.
Kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito cewa ya ce tsige sarakunan ya fara aiki ne daga yau Juma'a 20 ga watan Nuwamban shekarar 2018.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: