[post by samaila umar lameedo]
Kaduna Electric na kira ga wuraren ibadu dasu fara biyan kudin wuta bayan sun dauka kyauta ne
LABARAI DAGA 24BLOG
- Kamfanin wutar lantarki yayi kira ka coci da masallatai da su fara biyan kudin wuta
- Rashin biyan kudin ka iya sawa a yanke musu wuta
- Ya zama tilas su dinga biyan kudin duk wata
Kaduna Electric na kira ga wuraren ibadu dasu fara biyan kudin wuta bayan sun dauka kyauta ne
Kamfanin dake samar da wutar lantarki na Kaduna Electric shiyyar Kaduna, Sokoto, Kebbi da Zamfara yayi kira ga Coci-coci da masallatai dasu fara biyan kudin wutar lantarki da suke sha.
Abdulazeez Abdullahi, Daraktan bangaren sadarwa na kamfanin mai zaman kansa, yace rashin biyan kudin wutar ka iya sanyawa a yanke musu wuta, domin ana tafka asara kan wannan rashin biyan kudin wuta na mujami'un.
Da yake bayani yace "Kamfanin dake samar da wutar lantarki na Kaduna Electric yana kira ga shuwagabannin addinai (Limamai da Fastoci) dasu fara biyan kudin wuta kamar yadda kowa yake biya."
Idan har basu biya kudin ba to fa za'a fara yanke musu ita bisa tsarin kamfani, domin neman kudi ake ba kyauta ake samo wutar ba.
Bisa al'ada dai, a zamunnan da, kamfanin na wuta yana sayen wutar lantarki ne daga manyan kamfunna dake samar da ita watau GenCos, sannan ya raba ya sayar ya fidda riba, amma wasu basu son biyan kudin wutar.
Ana kuma yawan tsallake wuraren ibadu ko don kunya, da tsoron me kaaje-yazo, lokacin yankan wutar, su kuwa jama'a a wasu lokutan, kan taso ma da hayaniya, kan cewa wai ai wurin ibada ne ba'a isa a yanke masa wuta ba.
Hakan na yawan janyo wa kamfanin asara, musamman ganin suma wuraren ibadar, sukan amshi na fi-sabilillahi ko fi-sabili-Yesu a kullum daga masu ibada.
0 Comments:
Post a Comment