Tauraron fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello, General BMB na daga cikin masu goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa an mai tayin wasu kudi masu tsoka akan yabar Buhari amma yaki amincewa.
Bello yayi wannan maganane a lokacin da yake mayar da martani ga wata mata ta dandalinshi nasada zumunta da tace, akwai yunwa a mulkin Buhari, Bello yace mata, Wallahi sai Alah ya jarrabemu, mun dauki jarrabawar kafin jin dadi ya biyo baya.
Ya kara da cewa, wallahi na rantse an tayani miliyan 30 akan na daina tafiyar Buhari na ki amincewa saboda bana alaqa da mara gaskiya. Buhari Alkhairine mu kara hakuri
0 Comments:
Post a Comment