Rikicin 'yan Shi'a: Sojoji sun kafa hujja da Trump kan harbin 'yan Shi'a
LABARAI DAGA 24BLOG
Rundunar sojin Najeriya ta kafa hujja kan bude wa 'yan Shi'a wuta da wani faifan bidiyon na Shugaban Amurka Donald Trump, wanda a ciki shugaban yake cewa sojoji za su iya amfani da karfi kan baki 'yan ci rani da ke jifansu da duwatsu.
"Idan suka yi jifa da duwatsu... ku dauka sun yi da bindiga ne," in ji Mista Trump a wani faifan bidiyo.
Jami'an tsaron Najeriya sun kama mabiya Shi'a 400 bayan wani mummunan artabu na tsawon kwanaki a Abuja.
Kalli hotunan artabun 'yan Shi'a da sojoji a Abuja
Me Amurka ta ce kan rikicin 'yan Shi'a a Abuja?
Jonathan ya soki Buhari kan ci gaba da tsare Zakzaky
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta soki sojojin kasar da kashe 'yan Shi'a, inda kuma ta ce zanga-zangar 'yan Shi'ar ta lumana ce.
Sai dai mai magana da yawun sojojin kasar Burgediya Janar John Agim ya ce sun yi amfani da harsasai masu rai ne ga masu zanga-zanga saboda suna dauke da makamai.
Ya ce: "Wannan ne abin da Mista Trump yake magana a kai."
Shafin Twitter na rundunar sojin kasar ya wallafa bidiyon Shugaba Trump da rubutu kamar haka: "kalli wannan bidiyon, ka yanke hukunci".
Kakakin sojin ya ce sun wallafa bidiyon ne saboda mayar da martani ga rahoton kungiyoyin kare hakkin dan Adam da suke cewa sojoji sun yi amfani da makami kan 'yan Shi'a masu zanga-zanga.
Sai dai rundunar sojin ba ta yi magana game da sanarwar da ofishin jakadancin Amurka a Abuja ya fitar ba, inda Amurka ta bukaci gudanar da cikakken bincike da hukunta masu laifi a rikicin.
Ba za a iya tabbatar da yawan 'yan Shi'an da sojojin kasar suka kashe a Abuja lokacin artabun da aka kwashe tsawon kwanaki ana yi ba.
Sojoji sun ce mutum shida ne suka rasa rayukansu, amma 'yan Shi'an sun ce adadin ya wuce haka nesa, ita kuma kungiyar Amnesty ta ce adadin ya kai kimanin mutum 45.
Rikicin ya fara ne a lokacin da 'yan Shi'ar suka fara tattakin Arbaeen na shekara-shekara a Abuja - wato tarukan tunawa da kisan jikan Manzon Allah (SAW).
Har ila yau 'yan Shi'an suna neman sakin jagoransu Sheikh Ibrahim Zakzaky wanda ake tsare da shi kimanin shekara uku ke nan, bayan wani rikici da kungiyar ta yi da sojoji a Zaria.
Friday, 2 November 2018
Author: Anonymous verified_user
RELATED STORIES
MALAMAN ALKUR'ANI SUN YI JAN KUNNE GA TASHAR AREWA24 Cikin Shirin (DADIN KOWA)Muna kallon shirin dadin kowa Muna kallon yadda k
NJC zata sake dawowa a yau a kan Onnoghen, MuhammaduNJC zata sake dawowa a yau a kan Onnoghen, Muhamm
Atiku yace buhari Na Tsoron Mahawara DaniDan takarar Shugabancin Kasar nan karkashin peopl
Sojoji Sun Kashe wani agent name PDP A Jihar Rivers State (hotuna)Sojoji Sun Kashe wani agent name PDP A Jihar Rive
An Gano Manya Manyan Dalilan Da Suka Sa Atiku Ya Fadi ZabeA halin yanzu dai za a iya cewa karshen tika-tika
Yan Najeriya Sun Ganewa idanuwansu' Bullion Vans 'ana Shigar da gidan Tinubu a Bourdillon. 'Yan Najeriya Sun Ganewa idanuwansu' Bullion Vans
0 Comments:
Post a Comment