An sace wasu ‘yan mata tagwaye lokacin da suke kan hanyarsu ta kai wa ‘yan uwa da abokan arziki ankon bikinsu, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Mataimakin Shugaban karamar hukumar Zurmi Abubakar Muhammad ya ce tagwayen wadanda ake shirye-shiryen aurensu suna cikin mutane bakwai da aka sace a garin Dauran da ke jihar ZamfaraZamfara.
“A tsakanin ranakun Asabar zuwa Lahadi ne aka sace mutanen bakwai – wato maza hudu, mata uku.
“Nan kusa gare mu ma an sace namiji guda, mace guda wato nan Birnin Tsaba ke nan,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa: “A garin Moriki an ma an dauki mutum uku da wadansu da aka sace ciki har da wani kansila.”
Har ila yau ya ce an yi magana da masu garkuwa da mutanen kuma sun bukaci a “biya su naira miliyan 100 kafin su sako ‘yan tagwayen.”
Daga nan ya bukaci da a kawo musu dauki don kawo karshen matsalar.
Zamfara tana daya daga cikin jihohin arewacin kasar da ke fama da matsalar tsaro.
BBC HAUSA
Saturday, 10 November 2018
Author: Anonymous verified_user
RELATED STORIES
Yan Najeriya Sun Ganewa idanuwansu' Bullion Vans 'ana Shigar da gidan Tinubu a Bourdillon. 'Yan Najeriya Sun Ganewa idanuwansu' Bullion Vans
Customs na Nijeriya sun kama motoci 29, kayayyaki masu daraja N1.1bn a iyakar SemeCustoms na Nijeriya sun kama motoci 29, kayayyaki
SOjoji sun Kashe wata yar NYSC APC a cikin Bonny, Rivers State SOjoji sun Kashe wata yar NYSC APC a
Kaddamar da: Ayyukan IGP Adamu ya umarce su su rarraba FSARSKaddamar da: Ayyukan IGP Adamu ya umarce su su ra
ASUU Ta Janye Dogon Yajin Aikin Da Ta Shiga Tsawon Wata Uku Kungiyar Malaman Jami'o'i Nijeriya ASUU ta janye
Buhari Tamkar Uba Yake A Gare Ni, Ni Ba Makiyinsa Ba Ne, Cewar Sanata Dino MelayeDuk wanda ya sake kallona a matsayin makiyin Buha
0 Comments:
Post a Comment