Monday 3 December 2018




Abubuwanda za a gudanar a nigeria wannan satin

Home Abubuwanda za a gudanar a nigeria wannan satin

Anonymous

Ku Tura A Social Media

Yau ranar Litinin ce, kuma ita ce rana ta farko a wannan makon, don haka ya kamata mu dan yi hasashen wasu abubuwan da za su faru cikin kwanaki bakwai din makon masu zuwa, duk da cewa ba mu san ainihin abin da ke iya faruwa ba.

Ga dai wasu abubuwa masu muhimmanci da ake sa ran za su faru a duniya a wannan makon.
1 - Atiku zai kaddamar da yakin neman zabensa
A yau Litinin ne dan takarar mukamin shugaban kasa, Atiku Abubakar zai kaddamar da yakin neman zaben sa a birnin Sokoto da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Me ya sa aka damu da taron?

Atiku Abubakar shi ne dan takarar babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, wadda ta mulki kasar na tsawon shekara 16.

Dan takarar kuma ya taba rike mukamin mataimakin shugaban kasar Najeriya a karkashin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Atiku Abubakar ya kuma nada wasu matasa uku, wadanda za su taka rawa a kwamitin yakin neman zaben nasa..

A cikin wadanda ya nada hara da wata mata da za ta rike mukamin mai taimaka masa ta musamman a yankin kudu maso yammacin kasar.

Sauran sun hada da Dakta Ahmed Adamu da Aliyu bin Abbas da kuma Phrank Shuaibu.

2 - Tsoron karancin man fetur
Hakkin mallakar hoto Getty Images

Me zai faru?

Najeriya na fuskantar yiwuwar karancin man fetur.

Me ya sa aka damu da batun?

Masu dillancin man fetur a najeriya sun bai wa gwamnatin kasar wa'adin kwana bakwai domin ta biya mambobinta bashin da suke bin ta da yawansa ya kai naira biliyan 800.

Dillalan sun sha alwashin tsayar da ayyuka a dukkan wuraren da ake ajiye man fetur a fadin kasar idan gwamnatin ta kasa biya masu bukata.

Kamfanin mai, NNPC ne ke da alhakin shigar da man fetur da sauran albarkatunsa cikin kasar.

Amma kamfanin ya dogara ne ga wasu kamfanoni na 'yan kasuwa domin ajiyar man da rarraba shi a cikin kasar.

Saboda wannan ne ake ganin cewa za a fuskanci karancin man fetur a kasar idan kamfanonin 'yan kasuwa suka janye ayyukansu na rarraba man, musamman ma a wannan lokaci na karshen shekara.

3 - Ranar Bikin Masu Nakasa ta Duniya

Me zai faru?

Yau ce ranar da kasashen duniya ke biki domin duba batutuwan da suka shafi wadanda ke da matsalar nakasa.

Me ya sa aka damu da bikin?

Ana gudanar da biki a fadin duniya domin batutuwan da suka shafi masu nakasa. Bikin na kokarin samar da hanyoyin da za a taimakawa masu nakasa samun cikakken 'yanci da ci gaba a duka fannonin rayuwa.

Fannonin sun hada da na siyasa da zamantakewa da tattalin arziki da na al'adu.

Taken bikin na bana shi ne karfafa wa masu nakasa domin inganta rayuwarsu wajen cimma Shirin Bunkasa Rayuwar Al'umma mai Dorewa na shekarar 2030.

4 - Gwamnatin Sudan da 'yan tawaye za su rattaba hannu kan yarjejeniya
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dakarun Sudan a yayin da suke wani fareti domin girmama ministan tsaron Masar a Khartoum

Me zai faru?

Kungiyar Justice and Equality Movement (JEM) ta Sudan ta sanar da cewa za ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da gwamnatin Sudan a cikin makon nan a birnin Berlin na kasar Jamus.

Me ya sa aka damu da batun?

Wannan yarjejeniyar da gwamnatin Sudan da kungiyoyin JEM da kuma Sudan Liberation Movement - Minni Minnawi (SLM-MM) za su rattaba hannu a kai na karkashin wani shirin zaman lafiya tsakaninsu da aka kulla a Doha ta kasar Qatar ne.

Shugaban kungiyar JEM Jibril Ibrahim ya sanar da cewa kungoyin za su sanya hannu ranar 6 ga wannan watan na Disamba, a lokacin wata ganawa da yayi da manema labarai a birnin Paris.

Ana sa ran bangarorin za su tattauna a kan batutuwan da suka hada da shirin tabbatar da zaman lafiya a yankin Darfur da shirin kwance dammara da Tarayyar Afirka ke shiga tsakani.

An dai shafe shekaru ana rikici tsakanin gwamnatin Sudan da kungiyoyin yankin Darfur da suke neman a ba su 'yancin cin gashin kansu.

Rikicin ya janyo asarar dubban rayuka, kuma ana fatan wannan yarjejeniyar za ta kawo karshen rikicin baki dayansa.

5 - Za a gurfanar da 'yan awaren Kamaru a Kotu
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu magoya bayan kungiyar Ambazoniya mai neman ballewa daga Kamaru na zanga-zanga a gaban ofishin firai ministan Birtaniya

Me zai faru?

Wasu 'yan tawayen kasar Kamaru za su bayyana a gaban kotu ranar Alhamis 6 ga watan Disamba.

Me ya sa aka damu da batun?

Wasu 'yan tawayen kungiyar da ke neman 'yanci daga Kamaru wadanda aka kama su a watan Janairun 2018 a Najeriya za su fuskanci shari'a a karon farko.

A zaman farko da kotun za ta yi, za ta saurari karar Sisiku Ayuk Tabe da sauran wadanda ake tuhuma tare da shi ranar 6 ga wannan watan.

Mista Tabe ne shugaban wata kungiya mai sunan "Jam'iyyar Ambazoniya" mai amfani da harshen Ingilishi wadda kuma ke neman ballewa daga Kamaru.

Rikicin ya janyo tashin hankali a yankin, har ya kai ga ana asarar rayuka da aikata manyan laifuka da suka hada da sata da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: