Ma'aikatar Kula da Masallatai biyu masu daraja na kasar Saudiyya ta killace sa'a biyu inda ta bai wa masu nakasa damar yin dawafi su kadai a ranar Litinin.
Ma'aikatar ta yi hakan ne don nuna muhimmancinsu a ranar masu nakasa ta duniya wacce ta fado ranar 3 ga watan Disamba.
Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito sakataren ma'aikatar Mashour Al-Monaami, na cewa hakan na nuna yadda Masarautar kasar ke nuna muhimmancin wadannan mutane a cikin al'umma da kuma ba su hakkokinsu.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar ce domin mayar da hankali kan irin hali da kalubalen da masu nakasa ke ciki a kowane fanni na rayuwa a duniya.
Taken ranar ta bana shi ne: "Tallafawa mutane masu nakasa da kuma da kuma tabbatar da daidato.
Yawanci dai wajen dawafi na yawan cika da mutane ta yadda ko yaushe sai dai masu lalura ko masu nakasa su hau can sama su yi nasu dawafin.
Saudiyya ta kafa wasu dokoki tare da bayar da kulawa ga mutane masu nakasa.
Yayin da ake ci gaba da bikin ranar nakasassu ta duniya, masu wannan larura a Najeriya ma sun bukaci mahukunta a matakin jihohi da su yi doka irin wadda ke jiran sa-hannun shugaban kasa don inganta rayuwarsu.
Masu bukata ta musamman din suna da yakinin cewa dokar za ta taimaka wajen kawo karshen barace-barace a Najeriya, tare da kyautata rayuwarsu ta yadda za su ba gudunmowa wajen bunkasa kasar.
BBChausa.
0 Comments:
Post a Comment