Saturday, 15 December 2018




An saki 'yan awaren Kamaru 100 da Paul Biya yayi wa afuwa

Home An saki 'yan awaren Kamaru 100 da Paul Biya yayi wa afuwa

Anonymous

Ku Tura A Social Media

Fiye da fursunoni 100 'yan yankin da ke amfani da turancin Ingilishi na Kamaru da shugaban kasar Paul Biya yayi wa afuwa sun sami 'yanci bayan an sako su daga gidan kaso a ranar Asabar.

Wasu kotuna na musamman na soji ne suka sallame su da yammacin Jumma'a bayan da aka kammala shirin sakin fursunoni 289 da shugaban yayi wa afuwa.

Kotun da ke birnin Yaounde ce ta bayyana jerin sunayen mutum 100 cikin wadanda afuwar ta shafa, amma ba dukkansu a ka saka ba.

Kanar Abega Epse Eko, shi ne alkalin kotun sojin , kuma ya bayyana cewa za a saki sauran daga baya daga inda 'yan sanda da jandarmomi ke tsare da su.An ji fursunonin na rera waka cewa: "Mun sami 'yanci" a daidai lokacin da suke ficewa daga harabar kotun. Wasunsu sun shafe wata bakwai zuwa shekara biyu a tsare.

Akwai kuma wasunsu da ke da raunuka a jikinsu.Hukumonin Kamaru sun bi wasunsu har jihar Taraba da ke Najeriya ne, suka kamo su da tuhumar su 'yan ta'adda ne.

Wani manomi da ke cikin wadanda aka saki wanda shi ma an kamo shi a cikin jihar Taraba ne ya ce yayi farin cikin cewa zai yi bikin kirsimeti tare da iyalansa:

"Na san cewa wata rana za a sake ni. Abin da yayi min ciwo shi ne na rasa wata bakwai na rayuwata a banza," inji sh.

Ya kuma ce bayan fargabar wani abu saboda shi ya san bai aikata wani laifi ba.

Matsin lamba daga kasashen ketare musamman Amurka ce ta sa gwamnatin shugaba Paul Biya ta dauki matkin tattaunawa da 'yan awaren domin kawo karshen rikicin d yayi sanadin mutuwar mutane masu yawa

Share this


Author: verified_user

0 Comments: