Wednesday 5 December 2018




Bayan mummunar zanga-zangar adawa kasar Faransa ta janye karin farashin makamashi

Home Bayan mummunar zanga-zangar adawa kasar Faransa ta janye karin farashin makamashi

Anonymous

Ku Tura A Social Media
Fira Ministan Faransa Édouard Philippe ya sanar da matakin gwamnatin kasar na janye karin da ta yi kan farashin albarkun mai da kuma lantarki.


Matakin karin farashin dai, ya janyo kazamar zanga-zangar dubban 'yan kasar, lamarin da ya haifar da arrangama tsakaninsu da jami'an tsaro, musamman a birnin Paris inda aka kone dukiya mai tarin yawa.


Yayin sanar da janye karin, Fira Minista Edouard Philippe ya ce dakatar da karin zai kasance na tsawon watanni 6, kafin gwamnati ta yanke shawarar aiwatar da shi ko akasin haka, bayan gudanar da muhawara tsakanin wakilan gwamnati da jagororin masu zanga-zangar adawa da karin farashin albarkatun man.

Zuwa yanzu dai mutane uku suka rasa rayukansu, tun bayan da zanga-zangar ta juye zuwa tarzoma da barnata dukiya, yayinda kuma ‘yan sanda suka kama sama da mutane 500.
RFIhausa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: