Monday, 3 December 2018




Boko Haram: Me 'yan sanda 2,000 da karnuka za su yi a arewa maso gabas

Home Boko Haram: Me 'yan sanda 2,000 da karnuka za su yi a arewa maso gabas

Anonymous

Ku Tura A Social Media
[post by samaila umar lameedo]

Boko Haram: Me 'yan sanda 2,000 da karnuka za su yi a arewa maso gabas

LABARAI DAGA 24BLOG
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce za ta tura da karin 'yan sandan kwantar da tarzoma 2,000 da kuma kwararrun jami'anta kan yaki da ta'addanci tare da karnuka masu iya sansano abubuwa zuwa yankin arewa maso gabashin kasar.
Ta ce 'yan sanda za su taimaka wa sojoji a yakin da suke yi da 'yan kungiyar Boko Haram.
A wata sanarwa da kakakin 'yan sandan na Najeriya Jimoh Moshood ya fitar a ranar Lahadi, ya ce umarnin hakan wanda Supeto Janar na rundunar ya bayar, yana daga cikin tanadin aikin 'yan sanda domin tabbatar da zaman lafiya da bin doka da oda.
Boko Haram 'na kai wa sojoji hari da jirage marasa matuka'
'Yan sanda sun yi nasara kan barayin shanu a Zamfara
Mai bai wa babban supeton 'yan sandan shawara kan hulda da manema labarai Bala Ibrahim ya ce ssojoji na samun galaba a yakin da suke yi da Boko Haram kuma 'yan sandan za su je ne domin su taimaka mu su.
"Ba wai 'yan sanda ne za su je gaba ba, 'yan sandan za su je wurare ne da sojoji suka murkushe 'yan Boko Haram domin su tabbatar da zaman lafiya da doka da oda a wadannan wurare" in ji shi.
Hukumomin Najeriyar dai na daukar wannan mataki ne a yaki da 'yan Boko Haram a wannan lokacin da kungiyar ke sananta hare-hare a kan sojojin kasar a yanzu.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: