Da duminsa: Majalisar wakilai ta nada sabon karamin akawu
- LABARAI DAGA 24BLOG
A yau, Litinin, 3 ga wata ne majalisar tarayya ta amince da nadin Patrick A Giwa a matsayin mukaddashin karamin akawun majalisar.
Kafin nadinsa, Giwa ya kasance mataimaki ga karamin akawun majalisar da ya yi ritaya daga aiki a ranar Lahadi, 25 ga watan Nuwamba.
Sanarwar nadin Giwa na kunshe ne cikin wata sanarwa da Alhaji M A Sani-Omolari, babban akawun majalisar, ya aike ga dukkan ma su rike da mukami a majalisar.
Sanarwar ta ce, "majalisar wakilai ta amince da nadin Patrick A Giwa a matsayin karamin akawun majalisar wakilai na rikon kwarya, nadin ya fara aiki ne daga ranar 26 ga watan Nuwamba."
cewar akwai kwararan alamu da ke nuna cewar Uche Nwosu, tsohon shugaban ma'aikatan jihar Imo kuma suruki ga gwamna Rochas dake neman takarar gwamna a APC ya canja sheka zuwa jam'iyyar AA.
Hakan ta fito fili a bayyane ne bayan wayar gari da ganin fastocin Nwosu tare da na shugaba sun mamaye ko ina a jihar Imo.
Faruwar hakan ta kawo karshen duk wani hasashe da canki-in-canka a kan makomar surikin na Rochas bayan jam'iyyar APC ta hana shi tikitin takarar gwamna.
Majiyar mu ta shaida mana cewar an fara ganin fastocin Nwosu a garin Owerri tun yammacin jiya, Lahadi, 2 ga watan Disamba, ranar da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) za ta rufe karbar sunayen 'yan takarar gwamna daga jam'iyyu.
Rochas Okorocha ne ya kafa jam'iyyar AA kafin ya canja sheka zuwa PDP, sannan daga bisani ya koma APC.
A ranar 31 ga watan Janairu ne hukumar zabe za ta fitar da jerin sunayen 'yan takara a kowacce jam'iyya.
0 Comments:
Post a Comment