Dalilan PDP na kaddamar da kamfen Atiku a Sokoto
LABARAI DAGA 24BLOG
Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya PDP ta kaddamar da kamfe na dan takarar shugabancin kasa a karkashinta Alhaji Atiku Abubakar a birnin Sokoto da ke arewa maso gabashin kasar, a ranar Litinin.
Kamfe ne zai zama na farko na Atiku Abubakar a kasar, wanda aka fara ranar 3 ga watan Disamba.
A ranar Lahadi da yammaci ne jam'iyyar ta fitar da sanarwar gayyatar al'umma zuwa wajen kamfe din a shafinta na Tiwtter:
Shi ma Atiku Abubakar ya sanya a shafinsa na Twitter ranar Litinin cewa: "A yayin da muka fara kamfe dinmu na shiyya a yau, Ina son tunasar da 'yan Najeriya alkawurana da kuma ci gaban kasarmu na samar da ayuukan yi da hadin kai da kuma tsaro.
Dalilin da ya sa nake goyon bayan Atiku - Jonathan
Najeriya ta bai wa Amurka shawara kan Atiku Abubakar
Jam'iyyar PDP dai ta ce ta zabi fara kamfen din ne a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya saboda dalilai kamar haka:
Warware matsaloli
Mayar da hankali kan batutuwa da kuma warware damuwa da tsoro da matsalolin 'yan Najeriya da ke wannan yanki tare da biya musu bukatunsu kamar yadda yake a cikin tsare-tsaren da Atiku Abubakar ke son gabatarwa idan ya hau mulki.
Ganawa da shugabanni
Jam'iyyar ta ce za ta yi amfani da gangamin don ganawa da shugabannin al'umma na wannan yanki don ci gaba da tattaunawa don neman hadin kansu wajen "ceto kasar daga rashin iya shugabanci na Shugaba Muhammadu Buhari da kuma gazawar APC," kamar yadda PDP ta ce a sanarwar da ta fitar.
Buhari ya yi biris da Arewa maso yamma
Jam'iyyar PDP ta ci ga da cewa kwamitin kamfe din ya lura cewa Shugaba Buhari ya nuna halin ko oho ga yankin arewa maso yamma.
"Babu wani abu na ci gaba da APC da Buhari za su iya nunawa a yankin arewa maso gabas su ce aikinsu ne da suka yi cikin shekara uku da rabi dinnan," in ji sanarwar PDP.
A ganin PDP yankin bai yi tsammanin haka ba daga Shugaba Buhari, wanda "bai cika ko daya daga cikin alkawuransa na 2015 ba."
Neman hadin kan Arewa maso yamma
Wani dalili da PDP ta sake bayarwa shi ne na yadda ta yi ikirarin cewa gwiwar yankin arewa maso yamma ta yi sanyi dangane da Shugaba Buhari, don haka a yanzu "suna son bai wa Atiku BAubakar goyon baya, wanda ya nuna son ci gaba dawo da kasar madaidaiciyar hanya da kawo mata ci gaba."
Bayan kammala rattaba wadannan dalilai, sai kuma jam'iyyar PDP ta mika sakon godiya da addu'a ga al'ummar yankin arewa maso yamma kan goyon bayan da suka nunawa dan takararta Atiku Abubakar.
0 Comments:
Post a Comment