Dalilin da ya sa nake goyon bayan Atiku - Jonathan
Jonathan wanda ya taba yin hamayya da Atiku a jam'iyyar PDP ya shaidawa BBC cewa zai goyi bayan wanda ya san zai hada kan 'yan Najeriya.
"Ina goyon bayan wanda na yi imanin cewa, idan ya zama shugaban kasa zai tafi da kowa, Igbo da Yoruba da Fulani da Hausa da mutane na Ijaw da 'yan kabilar Tiv, duk zai tafi tare da mu"
"Idan ya ci, za mu san cewa dukkaninmu 'yan Najeriya ne." in ji shi
Ya kuma ce ya kamata mutane su san cewa PDP ta yi wa 'yan Najeriya aiki sosai, yana mai cewa "idan da ace PDP ba ta tsinana komi ba da yunwa ta kashe 'yan Najeriya."
"Wadanda ke cewa PDP ta yi wannan ta yi waccan, ni ban yadda ba. PDP ta yi iya nata kokari, wasu kuma sai su gwada nasu kokarin mu gani."
Jonathan ya kara da cewa babbar matsalar da ke damun Najeriya shi ne "idan ba mu yi da kyau ba za mu samu rabuwar kai."
Ya ce wasu za su mutu, wasu kuma dole su gudu su bar kasar. "Idan muka kasa hada kanmu, ba abin da za mu iya yi," in ji shi.
Goodluck Jonathan shi ne shugaban gwamnatin dimokuradiya na farko a Najeriya da ya sha kaye a zaben shugaban kasa.
Kuma ya sha yabo a ciki da wajen Najeriya kan yadda ya gaggauta amince wa da shan kaye tare da mika mulki ga Buhari na APC ba tare da wani tashin hankali ba.
0 Comments:
Post a Comment