Saturday 8 December 2018




Gwara na gudu daga Gida Akan A cutar da Messi _MURTAZA DANA SHEKARA 7

Home › › Gwara na gudu daga Gida Akan A cutar da Messi _MURTAZA DANA SHEKARA 7

Anonymous

Ku Tura A Social Media
Yaron nan dan kasar Afghanistan wanda ya yi suna a shafukan intanet saboda kaunar da yake yi wa fitaccen dan kwallon kafa Lionel Messi ya tsere daga gidansu karo na biyu sakamakon barazanar ‘yan Taliban. Sunan Murtaza Ahmadi, wanda yanzu shekararsa bakwai da haihuwa, ya bazu a duniya a shekarar 2016 bayan an dauki hotonsa sanye da rigar kwallon kafa da aka yi da jakar leda mai dauke da lambar da Messi ke sanya wa inda daga bisani ne ya gana da Messi a Katar. Iyayensa sun ce yanzu sun tsere daga gidansu da ke Afghanistan bayan kungiyar ‘yan ta’adda ta Taliban ta yi musu barazana kan rayuwarsu saboda dansu yanason dan wasa Messi wanda ba musulmi bane. Suna zaune ne a lardin Ghazni da ke kudu maso gabashin kasar – inda masu tayar da kayar baya ke hara – sannan suka tsere zuwa Kabul, babban birnin kasar domin tsira da rayuwarsu data dansu. Iyayensa sun taba neman mafaka ta wucin-gadi a Pakistan a 2016, amma sun koma kasarsu bayan kudinsu ya kare, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP. Murtaza yana dan shekara biyar a duniya lokacin da ya sanya rigar ta jakar leda mai launin shudi da fari irin wacce ‘yan wasan kwallon kafar Argentina inda Messi yake wa kyaftin suke sanya wa. Bayan hotonsa ya watsu a shafukan sada zumunta, mutane sun yi kira da a nemo shi domin ya gana da Messi sai dai lokacin da aka fitar da sunan yaron, dan kwallon kafar ya aike masa da sako – ciki har da rigarsa ta kwallon kafa wacce ya sanya wa hannu. Daga bisani ne Messi ya gayyaci Murtaza zuwa Doha domin su gana lokacin da Barcelona ta buga wasan sada zumunta a Doha a 2016. Yaron da kuma Messi sun shiga filin wasa tare.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: