Friday, 7 December 2018




Kalli yadda ake asiri da mujiya saboda siyasa

Home Kalli yadda ake asiri da mujiya saboda siyasa

Anonymous

Ku Tura A Social Media

Lokacin zabuka a Indiya, hukumomi na mayar da hankali ne wajen rarraba kayan masarufi da ake bai wa masu kada kuri'a a matsayin cin hanci.

Amma a wannan karon, Mujiyoyin Indiya ne hukumomin Karnataka su ke kokarin karewa daga fasa kwauri zuwa jihar Telangana da ke makwaftaka da Karnataka- inda za a gudanar da zabuka ranar Juma'a.

Mutum shida aka kama a Sedam, wacce take makwaftaka da jihar Telangana bisa laifin fasa kwaurin tsuntsayen, kuma sun bayyana wa masu bincike cewar ana matukar bukatar mujiyoyi.
Amma mallakar da sayar da mujiyar ta hanyar da ba ta dace ba babban laifi ne a Indiya karkashin dokar kare namun dawa.
Tsafi

Sai dai abun mamaki a nan shi ne, a wannan karon, ba amfani ake da mujiyoyi a matsayin cin hanci ba, a cewar wani jami'in 'yan sanda wanda ya tattauna da sashen Hindi na BBC.

Ana ganin cewar wasu sassan jikin mujiyar na janyo rashin sa'a ga dan takarar daya bangaren," a cewar jami'in.

Masu kada kuri'a dai za su zabi 'yan majalisun jihar ne ran 7 ga watan Disamba.
Hakkin mallakar hoto karnataka police
Image caption Wasu sun yadda cewa mujiya na iya janyowa dan adawa ya fadi zabe

Wani jami'in hukumar da ke kula da dazuka, Ramakrishna Yadav ya ce: "Wadanda ake zargi sun ce wani mutum ne daga Telanaana ya neme su ta waya, kuma ya shaida masu cewa ana bukatar mujiya don yi wa dan takarar bangaren adawa tsafi."

"Ana kuma amfani da mujiyoyi wajen haifar da tsoro ga bangaren adawa na cewar wani na amfani da tsafi don ya wargaza su. Wato dai a sa masu fargaba," a cewar Mr Yadav.

Wani dan sanda, wanda ba a ba shi izinin magana da manema labarai ba, ya shaida wa BBC Hindi cewa, "bin sahun wadanda ake zargin zuwa ga dan siyasar da ya sa su nemo mujiyar babban aiki ne."

"Ba mu sani ba ko dan siyasar ne ya ba su aikin ko kuma wani daban daga bangarensa."
Ana mukatar mujiya sosai

Indiya na da kusan dangin mujiya 30, amma an fi bukatar dangi biyu da su ka fi yawa a kasuwar bayan fage, inda ake siyar da su don yin tsafi.

Dakta Saket Badola, shugaban wata kungiya da ke sa ido kan saye da sayarwar mujiya ya shaida wa BBC Hindi cewa ba za a iya kwatanta girman matsalar saye da sayarwar mujiya ba a bisa ka'ida ba.

"Amma daga bayanan da mu ke da su, mun san cewa matsalar na da girma. Matsalar ta fi yawa a jihohin Arewa amma akwai ta ma a Kudancin kasar." in ji Dakta Badola.
Hakkin mallakar hoto karnakata forest dept
Image caption Ramakrishna Yadav ya ce ana amfani da mujiyoyi ne a Indiya wajen yin tsafi
Farce, jini da bakin tsuntsu

Dakta Asad R Rehmani, tsohon darekta a Hukumar Tarihi ta Bombay ya bayyana wa BBC Hindi cewa:"Ana amfani da farcen yatsun kafa, da jini da bakin tsuntsun ta hanyoyi da dama a yankuna daban-daban."

"Yankuna da dama na ganin mujiya a matsayin wata aba mai dauke da rashin sa'a saboda tana rayuwa a wurare masu duhu, wadanda babu kowa a cikinsu, kuma hakan ba gaskiya ba ne."

Wata jami'a a Hukumar Kare Namun dawa, Sharath babu ta ce wahalar da mujiyar ake yi idan za a yi tsafin da ita.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana amfani da wannan dabbar da kunkuru wajen tsafe-tsafe

Mr Babu ya sha ganin an soka wa dabbobi allurai a idanuwansu ko kuma fuka-fukansu a karye.

"Idan wani yana so ya ci galaba a kan wani, sai a daura kyallen kayansa a jikin mujiya sai a jefar da ita a gaban gidan wanda aka yiwa

Share this


Author: verified_user

0 Comments: