Tuesday 4 December 2018




Ma'aikatan Kananan Hukumomin Jihar Zamfara Na Amsar 6,000 A Matsayin Mafi Karancin Albashi

Home Ma'aikatan Kananan Hukumomin Jihar Zamfara Na Amsar 6,000 A Matsayin Mafi Karancin Albashi

Anonymous

Ku Tura A Social Media


Shugaban kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi na kasa (NULGE), Ibrahim Khalil, ya ce ma'aikatan kananan hukumomin jihar Zamfara na amsar naira dubu shida (₦6,000) a matsayin mafi karancin albashi. Hakan ya sa ma'aikatan sun zamo na karshe a yawan albashi a gaba daya Nijeriya.


Ibrahim Khalil ya bayyana hakan a birnin Habuja yayin da taron bikin cikar kungiyar shekaru 40 da kafuwa. 

A dangane da rahoton kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN), kin biyayyar da gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, yayi ga dokar da ta umarci kowanne gwamna kan ya biya naira dubu sha takwas (₦18,000) a matsayin mafi karancin albashi ce ta zamo babban dalilin da ya sanya yake jayayya da yunkurin karin mafi karancin albashi zuwa naira dubu talatin (₦30,000). 

Khalil, wanda kuma shi ne ma'ajin kungiyar 'yan kwadago (NLC) na kasa, ya kara da fadin cewa karancin samun da mutanen Zamfara ke fama na daya daga cikin abubuwan da ke kawo karuwar rashin tsaro a jihar.

Shugaban ma'aikatan ya bayyana cewar kin biyan ma'aikata hakkokinsu yadda ya kamata zai iya haifar da rashin kwanciyar hankali a jihar.
Sarauniya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: