Dan takarar shugaban Najeriya a jam'iyyar PDP a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, ya zargi jam'iyyar APC mai mulkin kasar da sayen katunan zabe.
Sai dai APC ba ta ce komai a kan zargin ba.
Atiku ya yi zargin ne a birnin Ilorin na jihar Kwara inda ya kaddamar da yakin neman zabensa na shiyyar arewa ta tsakiyar kasar ranar Laraba.
Tsohon mataimakin shugaban na Najeriya ya ce "Wannan shi ne abin da APC take yi. Tana sayen katunan zabe, za ta zo wurin ku ta ba ku N10, N20 ko kuma N50 domin sayen katin zabenku - suna sayen makomarku. Shin kuna so ku sayar da makomarku? Kada ku sayar da katin zabenku domin za a yi amfani da su wajen musguna muku."
Tsallake Twitter wallafa daga @atiku
This is what the APC are doing. They are buying PVCs, they will come to you and give you N10, N20, N50 to buy your PVC - they are buying your future. Do you want to sell your future? Don’t sell your PVCs because they are going to use it against you. #PDPNorthCentralRally
— Atiku Abubakar (@atiku) 5 Disamba, 2018
Karshen Twitter wallafa daga @atiku
Hotunan kaddamar da yakin neman zaben Atiku Abubakar
Atiku ya kaddamar da shirin 'ceto Najeriya daga kangi'
Alhaji Atiku Abubakar ya yi zargin cewa cin hancin da ake yi a gwamnatin Shugaba Buhari ya fi wanda ya faru lokacin mulkin tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan.
"Kazalika a tarihinmu ba a taba fuskantar matsalar rashin tsaro kamar a wannan lokaci ba," in ji dan takarar na PDP.
Da ma dai a makon jiya, shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya zargi gwamnatin Buhari da yin amfani da shirin nan na tallafawa kananan 'yan kasuwa da jari, TraderMoni, wajen sayen katin zabe.
0 Comments:
Post a Comment