Manyan aminan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano Rabi'u
Musa Kwankwaso sun fice daga jam'iyyar PDP inda suka
koma APC.
Wasu hotuna da mai taimaka wa shugaban Najeriya,
Muhammadu Buhari, kan hanyoyin sadarwa na zamani, Bashir
Ahmad, ya nuna aminan Kwankwaso irin su Farfesa Hafiz
Abubakar da Aminu Dabo - tsohon shugaban hukumar kula ta
tasoshin jiragen ruwan Najeriya - a fadar shugaban kasa ranar
Alhamis da daddare.
"Shugaba Buhari ya yi maraba da wasu jagororin siyasar jihar
Kano, cikin su har da Farfesa Hafiz Abubakar, tsohon
mataimakin gwamna jihar wadanda suka komo jam'iyyarmu
mai girma bayan sun fita daga wata jam'iyya," in ji Bashir
Ahmad.
Da ma dai tun a farkon mako ne ake rade-radin cewa 'yan
siyasar za su fita daga PDP su koma APC.
A watan Oktoba ne Farfesa Hafiz ya fita daga APC bayan ya
gaza samun takarar gwamna a jam'iyyar.
Sai dai a wata wasika da ya aike wa shugaban jam'iyyar na
mazabarsa ta Mandawari, Farfesa Abubakar, ya ce ya fita daga
jam'iyyar ne domin radin kansa.
A watan Agusta ya sauka daga kujerar mataimakin Gwamna
Abdullahi Umar Ganduje sannan ya fice daga jam'iyyar APC ya
koma PDP inda uban gidansa, Sanata Kwankwaso yake.
Sai dai daga bisani ya koma PDP inda ya nemi tsayawa takarar
gwamnan jihar a inuwar jam'iyyar.
Zabukan fitar da gwanin da aka yi a jam'iyyar reshen jihar
Kano sun bar baya da kura sakamakon tsayar da Malam Abba
Yusuf - surukin Sanata Kwankwaso - a matsayin mutumin da
zai yi takarar gwamna a PDP.
Rahotanni sun ce wannan mataki bai yi wa wasu jiga-jigan
jam'iyyar a jihar dadi ba, cikinsu har da Farfesa Abubakar,
wanda ya yi tsammani shi za a tsayar a matsayin dan takara.
0 Comments:
Post a Comment