Saturday 1 December 2018




MATASAN DA SUKAYI KIDAYAR BUHUN GERO SUN FITAR DA SAKAMAKO

Home MATASAN DA SUKAYI KIDAYAR BUHUN GERO SUN FITAR DA SAKAMAKO

Anonymous

Ku Tura A Social Media

Yanzu haka an kammala bikin bayyana sakamakon kidayar buhun gero a garin Yauri dake jihar Kebbi, wanda wasu matasan garin Yauri sukayi kirga kuma yau sun bayyana sakamakon ko kwara nawa ke cikin buhun gero.
Babban bako mai jawabi shine Farfesa Aliyu Muhammad Bunza kuma ya yi jawabi mai gamsarwa da kuma jinjinawa wadannan matasa.
Sannan mai martaba Sarkin Yauri Dr. Zayyanu Abdullahi shi ma ya yi jawabi a wurin bikin inda shi ma ya yi yabo da jinjina ga matasan, inda ya kara da cewa wannan aiki na kidayar buhun gero tamkar maganin zaman banza ne idan aka yi la'akari da duk matasan da suka yi wannan aiki suna da sana'ar yi.
Kuma bikin ya samu wakilcin Maigirma Gwamnan Jihar Kebbi Sen. Atiku Bagudu wanda Kwamishinan yada Labaru na Jihar Kebbi Hon. Gado Marafa ya Wakilta. Inda ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kebbi shirye take ta taimakawa matasan Jihar Kebbi da duk wani aikin alheri da suka kirkiro don daga martabar Jihar Kebbi da kuma Nijeriya a idon duniya.
Milyan goma sha daya, da dari tara da saba'in da tara, da dari takwas da sittin da takwas(11,979,8
68) ke kicin buhun gero.
Miliyan biyu, da dari uku da casa'in da biyar, da dari da saba'in da uku, da kwara shida (2,395,973,6 ) kowane damin gero.
Matasan su 37 ne, sun yi kwana 107 wajen kidayar buhun geron.
Daga karshe shahararren mawakin Masarautar Yauri Alh. Ibrahim Sani Dandawo shima ya yi waka akan bikin kidayar buhun gero a garin na Yauri.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: