Saturday, 8 December 2018




Mene ne makomar Lukaku da Hazard da Neymar da kuma Mbappe

Home Mene ne makomar Lukaku da Hazard da Neymar da kuma Mbappe

Anonymous

Ku Tura A Social Media
[post by samaila umar lameedo]

Mene ne makomar Lukaku da Hazard da Neymar da kuma Mbappe

LABARAI DAGA 24BLOG
Dan wasan gaban Belgium Romelu Lukaku, mai shekara 25, yana tunani game da makomarsa a Manchester United bayan ya ji takaicin salon jagorancin koci Jose Mourinho, in ji
(Sun) .
Jaridar (Mirror kuwa ta ambato Mourinho yana cewa Manchester United ba ta da damar cin kofin gasar Firimiya nan kusa idan Manchester City da Liverpool suka cigaba da kashe kudi.
Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce shi ba zai nemi dan wasan tsakiyar
Chelsea da kasar Belgium Eden Hazard, mai shekara 27, ba, in ji (Standard).
(L'Equipe ta ba da rahoton cewar Paris St-Germain ta shirya ta sayar da dan wasan gaban Brazil striker Neymar, mai shekara 26, ko kuma dan wasan gaban Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 19, don kauce wa ladaftarwar hukumar da ke tabbatar da cewa kungiyoyin kwallon kafa ba su kashe kudin da ya ya fi samunsu ba, wato Financial Fair Play (FFP).
Amma kungiyar ta PSG ta musanta labarin, kuma ta zargi L'Equipe da neman daukar fansa a kan kulob din, (PSG - in French) .
Jaridar De Telegraaf ta ruwaito cewar dan wasan tsakiyar Ajax Frenkie de Jong, mai shekara 21, yana fi son ya koma PSG fiye da Manchester City a wannan lokacin zafin , kuma kungiyar ta Faransa ta shirya domin biyan kudin yuro miliyan 75 don sayen dan wasan na kasar Netherlands.
Har ila yau jaridar (Sun ta ba da rahoton cewar dan wasan daManchester United da Chelsea ke hako Alex Sandro ya rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya a
Juventus . Dan wasan Brazil din mai shekara ya shirya domin cigaba da kasancewa a Tyurin har zuwa shekarar 2023.
Wolves za ta kashe kudin ba ta taba kashewa ba kan dan wasa ba inda za ta biya yuro miliyan 38 domin mayar da dan wasan Mexico mai shekara 27 da ke buga mata wasan aro daga kungiyar Benfica , Raul Jimenez, ya koma buga mata wasan dindindin, in ji (O Jogo - in Portuguese) .
Kafar (Liverpool Echota ruwaito cewar zai yi wuya Liverpool ta yi wa dan wasanta Harry Wilson, mai shekara 21, daga wasan aron da yake bugawa a Derby a lokacin kasuwar musayar 'yan wasa ta watan Janiru duk da jinyan da 'yan wasan Liverpool ke fama da su da kuma cigaban da dan wasan ya samu a inda yake buga wasan aro.
Kocin Arsenal Unai Emery ya ce ba zai yi wa 'yan wasa hudun da aka nuna suna shakar iskar nitrous oxide domin an yi bikin ne kafin a fara wannan kakar, in ji
(Sun) .

Share this


Author: verified_user

0 Comments: