Saturday 8 December 2018




Ministar Kudi Ta Jagoranci Zama Don Kirkiro Da Sabuwar Hanyar Samun Kudin Shiga Ga Nijeriya

Home Ministar Kudi Ta Jagoranci Zama Don Kirkiro Da Sabuwar Hanyar Samun Kudin Shiga Ga Nijeriya

Anonymous

Ku Tura A Social Media
A kokarin da Nijeriya ke yi na kirkiro da wasu hanyoyi da ba
na man fetir ba don samun karin kudaden shiga, Ministar Kudi
Zainab Shamsuna Ahmad a yau ta gana da jami'an kamfanin
'African Natural Resources and Mines Limited', wanda Mr.
Raji Gupta ya jagoranta, don zuba jarin Dala Miliyan Dubu
Dari Shida ($600m) a harkar tono ma'adanai da karafa a
karamar Hukumar Kagarko dake Jihar Kaduna.
Kimanin shekara ashirin kenan rabon da a samu yarjejeniyar
zuba jari irin wannan mai girma a fannin ma'adanai. Za'a
dinga samar da ton miliyan biyar da dubu dari hudu (5.4m) na
ma'adanai a kowace shekara; sannan aikin zai samar da
aikin yi ga dubun-dubatar 'yan Nigeria.
Bangaren samar da karafa na aikin zai maida hankali ne akan
tono tama da karafa, tare da sarrafasu zuwa nau'in karfen da
aka fi bukata wajen kere-kere.
Har ila yau, aikin zai samar da wutar lantarki mai karfin
megawatt 36 wanda hakan zai taimaka wajen inganta wutar
lantarki a karamar Hukumar Kagarko don bunkasa
masana'antu tare da kawo cigaba a yankin. Sannan za a
karkatar da rarar wutar da aka samu zuwa Rumbun Samar da
Lantarki na Tarayya don amfanar kasa baki daya.
Ko shakka babu, wannan aiki ne da zai bunkasa
masana'antu da kawo cigaba da samar wa jama'a aikin yi da
rage shigo da kaya daga waje da kawo ci gaban tono karafa
wanda hakan zai kawo alheri ga yankin tare da bunkasa
bangaren tono ma'adanai.
Rariya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: