Uwargidan Dan Takarar shugaban
kasa a karkashin jam’iyyar PDP
Hajiya Titi Abubakar Ta Bayyana
cewa Matsalar Talauci Da Rashin
Aikin Yi Da Gwamnatin Buhari Ta
Haddasa Ya Taimaka Wajen Karuwar Mace-macen Da Ake
Fama Da Shi A Kasar Nan.
Hajiya Titi ta kara da cewa zaben
mijin nata a matsayin shugaban
kasa a 2019 zai taimaka wajen
farfado da tattalin arzikin kasar
nan. Titi Abubakar ta bukaci ‘yan
Najeriya da suyi amfani da damar
da ke hannun su wajen kawar da
Gwamnatin mugaye da maye
gurbin su da ‘yan kishin Kasa,
domin dawo da Najeriya cikin hayyacin ta.
0 Comments:
Post a Comment