Wednesday 5 December 2018




SHIN DAGASKE MARYAM BOOTH TA AURI SADIQ ZAZZA6I

Home SHIN DAGASKE MARYAM BOOTH TA AURI SADIQ ZAZZA6I

Anonymous

Ku Tura A Social Media
Ana ce-ce-ku-ce kan wasu hotuna da fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood Maryam Booth ta wallafa na bikin aure.
Jarumar ta wallafa hotunanta tare da Sadiq Zazzabi mawakin Hausa kamar ango da amarya, hotunan da ke nuna kauna da soyayya.
Hotunan sun ja hankalin mabiyanta da ma'abota fina-finan Hausa.
An ta yada hutunan a shafukan sada zumunta na intanet cewa Maryam Booth za ta yi aure.
Wasu na tunanin a fim ne, yayin da wasu ke cewa da gaske ne za ta auri Sadiq Zazzabi ganin cewa mawaki ne da ba ya fitowa a fim.
BBC ta tuntubi Maryam Booth domin tabbatar da ko da gaske ne za ta auri Sadiq Zazzabi.
"Ban yi aure ba, a wani fim ne da ake kan shirya wa," in ji ta.
Ta kara da cewa an dauki hotunan ne a wani fim mai suna Gidan Biki na hudu da suka fito tare da mawakin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: