Shugaba Muhammadu Buhari ya sha ihu a majalisar dokoki yayin da yake jawabi kafin gabatar da kasafin kudi na shekarar 2019.
Shugaban ya sha tafi daga magoya bayansa amma 'yan adawa sai ihu suke suna cewa 'karya ne' yayin da yake jawabi kan nasarorin gwamnatinsa a majalisar da jam'iyyar PDP ke jagoranta.
Shugaban ya isa majalisar tare da ministocinsa kuma an yi tafi na cewa 'sai baba' da kuma sowa lokacin isowarsa.
Shugaban dai na gabatar da jawabi gaban 'yan majalisar wakilai da 'yan majalisar dattawan kasar ne da kuma ministocinsa da gwamnoni.
Sai dai wasu 'yan majalisar na yi masa ihun rashin amincewa da bayanin ayyukan da ya ce gwamnatinsa ta yi a fadin kasar.
Wasu 'yan majalisar kuwa suna yi masa tafi tare da furta kalaman karfafa masa guiwa.
Wednesday, 19 December 2018
Author: Anonymous verified_user
RELATED STORIES
Wata sabuwa- atiku abubakar ya bayyana abinda gomnatinshi bazata amince dashiba inyaci zabeDan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Al
INEC Ta Bi Umurnin Kotu Ta Anshi Yan Takarar Jam'iyyar APC Na Jihar ZamfaraHukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayy
An Gano Manya Manyan Dalilan Da Suka Sa Atiku Ya Fadi ZabeA halin yanzu dai za a iya cewa karshen tika-tika
Wani tsoho dan shekara 70+ ya auri yar shekara 15 Wannann lamarin wanda yaja hankalin jama sosai mu
Karamin Yaro mai shekara 8 dayake samun dala miliyan 22 ta intanet Wani yaro mai shekara takwas wanda ke yin bayani
Bazanyiwa atiku abubakar yakin neman zabe ba inji obasanjo- Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi kira kan za
0 Comments:
Post a Comment