Tuesday, 11 December 2018




TALLAFIN ABINCI DAGA KASAR SAUDIYYA ZUWA NIGERIA

Home TALLAFIN ABINCI DAGA KASAR SAUDIYYA ZUWA NIGERIA

Anonymous

Ku Tura A Social Media
Bahaushe ya yi gaskiya da ya ce, wanda ya san ka shi ne naka. Lallai haka ne, wanda ya tare da kai a lokutan wuya da dadi shi ne naka, domin shi ne ya gaskata tarayyar sa da kai, kuma ya damu da halin da kake ciki. Haka wanda ya taimaki wani a lokacin bukata, Allah zai taimake shi a lokacin nasa bukatar.
Kasar Saudi Arabia ta yi fice a tsakanin kasashen duniya wurin kyauta, tausayi da bayar da tallafi, wadannan kyawawan halaye sune dabi'un mutanen kasar Saudia da tsarin gudanar da gwamnatin kasar. Wadannan halayen 'dan adamtaka, tausayi da sanin ya kamata su suka sanya kasar Saudia a matsayin kasa ta biyu a jerin kasashe mafiya bayar da agaji da tallafi wa kasashen da ke cikin bukata. Wannan halin taimakon mabukata yana daga cikin karin dalilai da suka a kullum kasar ke samun taimakon Allah wurin kara ma ta ci gaba, daukaka da daraja a tsakanin kasashe.
Ranar Laraba da ta gabata, 5/12/2018 rana ce a mai cike da tarihi a kasar Nigeria, domin rana ce da gwamnatin Nigeria da 'yan gudun hijirar yakin Boko Haram na cikin gida ba za su manta ta ba, saboda a ranar ne ta kaddamar da rabon tallafin kayayyakin abinci, buhhunan shinkafa da wake da garin Semovita da wasun su da suka haura dubu dari da arba'in da dari hudu da sittin da takwas (140,468), kayayyakin da aka shirya raba wa iyalai kimanin dubu dari takwas da arba'in (840,000) wadanda suke tsugune a sansanonin 'yan gudun hijira da wasu garuruwa a tsakanin jihohin Borno da Yobe.
Wannan tallafi ya zo ne daga cibiyar Tallafin Jin Kai Da Agajin Gaggawa na Sarki Salman, wacce aka fi sani da sunan "King Salman Humanitarian Aid & Relief Centre (KSRelief)" tallafin da ya zo bayan da babban ministan tsaron Nigeria, Brigadier Gen. Mansur Dan Ali (rtd) ya nemi agajin gwamnatin kasar Saudia a watannin baya. Tallafin da tunin ya shiga hannun Hukumar Agajin Gaggawa (NEMA), wanda ranar Larabar da ta gabata ta yi bikin kaddamar da rabon sa akan idon manyan jami'an gwamnatin Nigeria da suka hada da gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima da babban Ministan Tsaron Kasa, Brigadier General Mansur Dan Ali (rtd) a sansanin da aka wa suna "Teacher Village" da ke garin Maiduguri na Jihar Borno.
An kaddamar da fara rabon kayayyakin akan idon shugaban tawagar wanda shi ne mataimakin daraktan bayar da agajin gaggawa na cibiyar ta KSRelief, Mr. Naseer Alsubai'i da 'yan tawagar sa, a karkashin jagorancin shugaban cibiyar NEMA na kasa, Malam Mustapha Maihaja, shugaban da alhakin kula da tallafin da rabon su ya ratayu a karkashin hukumar sa tare da hadin gwiwa da hukumomin Agajin Gaggawa (SEMA) da wasu cibiyoyi da hukumomi a jihohin da abun ya shafa.
ADADIN KAYAYYAKI
1. Buhun Shinkafa Da Wake = 125,372
2. Pakitin Buhun Garin Semovita, Gishiri, Mangyada, Maggi da Tumatirin Leda = 62,686
TUNA BAYA
Wannan tallafi ba shi ne na farko ba, a farkon watan Maris (March) na wannan shekara 2018, gwamnatin Saudia ta hannuu wannan cibiya na KSRelief ta kawo tallafin kudade da kayayyakin abinci masu gina jiki da kayayyakin kula da lafiya da karatu na kimanin USD 10million wa gwamnatin Nigeria domin tallafawa 'yan gudun hijiran da yakin Boko Haram ya daga su daga matsugunan su.
NAKA SHI NE NAKA
Tun daga fara yakin 'yan ta'addan Boko Haram zuwa yau, babu wata kasar duniya da ta kawo daukin tallafi mai tsoka da ya kai wannan tallafi da gwamnatin kasar Saudi Arabia ta kawo wa gwamnati Nigeria domin rage nauyi da radadi wa gwamnatin da 'yan gudun hijirar cikin gida. Wannan ke kara tabbatar da alakar gaskiya, kauna da tausayin gwamnatin Saudia akan al'umar Nigeria, tare da tabbatar manufar wannan cibiya ta KSRelief na bayar da tallafi da agajin jin kai ga wanda ya cancanta ba tare da la'akari da jinsi, nahiya, siyasa ko addinin mabukaci ba.
Lallai wannan dauki ya nuna gwamnatin Saudia ba ta siyasantar da jinanen raunana da mabukata da ke cikin yaki ko bala'i, domin idan da siyasa take yi da ire-iren wadannan yanayi da sai a ji ta tana tayin kawo sojoji mashawarta a fagen yakar 'yan ta'adda wa gwamnatin Nigeria, musamman lura da tafi gwamnatin Nigeria kwarewa a wannan fagen, domin ta riga ta fara dandana ta'addancin hare-haren masu tsattsauran ra'ayin addini a cikin gida. Hakika wannan gagarumin tallafi ya kara nuna mana gwamnatin Saudi Arabia ita ce abokiyar tafiyar al'umar Nigeria a cikin dadin da wuya, ta nuna damuwar mu damuwar ta ce.
FATA DA TUKWICI
Bahaushe ya ce kyawun kyauta tukwici, kuma lallai wannan kyauta ta cancanci tukwici, saboda haka muke bayar da shawari wa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da ta duba yiwuyar sanya sunan Sarki Salman wa mafi girman sansanin 'yan gudun hijira domin nuna godiya da tuna wannan gagarumin tallafi da kara yaukaka alakar kasashe biyun.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: