Najeriya ta lashe gasar cin kofin kwallon kafa ta mata ta 2018 da aka yi ranar Asabar bayan ta doke kasar Afrika ta kudu da ci 4-3 a bugun fenareti a wasan karshen da suka yi a birnin Accra.
Kasashen biyu sun tashi canjaras bayan da suka yi minti 120 suna wasa, inda mai tsaron gidan Najeriya Tochukwu Oluehi ta kare kwallon da Linda Motihalo ta Afrika ta kudu ta buga.
Tun da farko, 'yar wasan tsakiya Asisat Oshoala ta baras da kwallo a bugun fenareti.
Tawagar kwallon kafar ta Super Falcons, wadda ta je Ghana domin ta kare kabunta, ta sake nuna cewa ruwa ba sa'an kwando ba ne a gasar cin kofin kallon kafa ta mata, inda ta dauki kofin a karo na 9.
Da farko bangarorin biyu sun rika kokarin ganin cewa sun sha gaban juna.
'Yan wasan Afrika ta kudu sun rika kai kora gidan Najeriya, ko da yake 'yan wasan baya sun dakile hare-haren da aka rika kai ma su.
Hakkin mallakar hoto BBC Sport
Image caption Kyaftin din Najeriya Rita Chikwelu rike da kofin
Sai dai bayan minti 20 ana taka leda, 'yan wasan Najeriya sun farga, sai Asisat Oshaola ta kasa saka kwallon da Ngozi Okobi ta buga mata a cikin raga.
Yadda bugun fenareti ya kasance
Da farko yan wasan Najeriya sun fara buga wasan fenareti din ne ba tare da samun nasara ba, inda kwallon da Onome Ebi ta buga ba ta shiga raga ba. Sai dai Noko Matlou ta yi nasarar zura kwallo a cikin ragar tawagar Banyana Banyana.
Rita Chikwelu ta samu nasara a kwallon da ta buga, sai dai Mpumi Nyandeni ta farke wa kasarta.
Chinwendu Ihezuo ta sake samar wa Najeriya nasarada ci 3-2 , yayin da Mamello Makhabane ita ma ta saka kwallo a cikin ragar Najeriya .
0 Comments:
Post a Comment