Thursday, 3 January 2019




Ana Wahala a wasu yankunan arewacin Najeriya

Home Ana Wahala a wasu yankunan arewacin Najeriya

Anonymous

Ku Tura A Social Media

A arewa maso gabashin Najeriya shugabanin matasan yankin ne suka koka kan rashin isasun kayyayakin agaji ga jama'ar yankin daga gwamnatin da kungiyoyin agaji ke ikirarin cewa suna aikawa zuwa wasu yankin.

Rashin samar da abubuwa more rayuwa a wasu sassa a arewa maso gabashin kasar na kara jefa jama'ar yankin cikin kuncin rayuwa.

Shugaban matasan yankin Alhaji AbdurRahman Buba Kwacham yace akwai tayar da hankali hali da yanayin da yaga al'umma na rayuwa a garuruwan Michika, Madagali, Gulak da kuma Limakara saboda rashin dauki walau daga bangaren gwamnatin jaha ko kuma ta tarayya da ke ikirarin cewar sun kaiwa.

Yace ya kamata idan hukumomin Najeriya basu san abun da ke faruwa ba to ya kamata ace sun bincika dan ganin cewar an fitar da mutanen daga matsananciyar rayuwa, inji AbdurRahman Buba KwachamHar ila yau Kwacham yace akwai karancin ruwa, abincin, da kuma rashin ingantatun asobotoci, inda sama da shekarar bakwai babu wani jam'in gwamnati da ya ziyarce su ko kum ama aje ace za'a ga a wane hali suke.

''Baza'a ce gwamnati ko kungiyoyi basa kokari ba, amma sai dai ina kira ga gwamti da cewar tayi bincike, sannan kuma ta waiwayi al'ummar wadan nan yankuna, dan gurin in kaje sam kamar ma ba yanki Najeriya ba, babu wani abun more rayuwa, wanda dukkan mai imani sai ya tausaya musu'', a cewar AbdurRahman Buba Kwacham.

AbdurRahman Buba Kwacham ya kuma ce ya kamata ace shugaban hafsan sojin Najeriya ya kafa wani kwamiti ya bincika halin da ake ciki a yankin, dan in kaga mutane suna cikin ukuba, sannan babu wani jami'in gwamnati da ya taka kafar sa a wajen tsahon shekaru bakwai. in ji

#bbchausa

Share this


Author: verified_user

0 Comments: